Tashin bama bamai a Amirka | Labarai | DW | 16.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bama bamai a Amirka

Wasu jerin bama bamai sun tarwatse a yayin wasu wasannin gudun tsere da aka yi a Boston na Amirka inda akalla mutane 3 suka kwanta dama yayinda sama da 100 suka samu raunika

Rahotani daga Boston dake arewa maso gabashin Amirka, sun tabbatar da tashin wasu bama bamai guda biyu a jiya da yamma inda suka yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 3 yayin da sama da mutun 100 suka samu munayen raunika galibinsu yara da mata a tsakiyar birnin .
Bama baman sun tarwatse ne a bainar jama'a a gefen wata hanya a dai dai lokacin da wasu masu gudun tsrere ke wasaninsu, inji Ed Davis shugaban hukumar 'yan sandan birnin na Boston.
Wani mai magana da yayun fadar White House ta Amirka ya kira tashin bama baman da wani harin ta'addanci, to sai dai kawo yanzu babu wata alamar da ke tabbatar da harin ko na ta'addanci ne.
Jim kadan bayan harin shugaba Barack Obama ya nuna juyayi da kuma alhininsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Wannan dai shi ne hari na farko da ya faru a kasar ta Amirka tun bayan hare haren 11 ga watan Satumba da suka wakana wadanda kungiyar Alka'ida ta dauki alhakin kaiwa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu