Tashin bama bamai a Afghanistan | Labarai | DW | 12.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashin bama bamai a Afghanistan

Harin kunar bakin wake ya hallaka 'yan sandan Afghanistan biyu.

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam inda ya hallaka 'yan sandan kasar Afghanistan biyu da sanyin safiyar wannan Asabar (12. 10. 13). Wannan ya nuna rashin tsaron da kasar ke ci gaba da fuskanta, a daidai lokacin da dakarun kasa da kasa ke neman janyewa ddaga kasar.

Kakakin gwamnan gundumar Nangarhar ya tabbatar da faruwan lamarin.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya kai ziyara Kabul babban birnin kasar, domin duba yadda harkokin tsaro za su kasance bayan janyewar dakarun kasashen duniya a karshen shekara mai zuwa ta 2014.

Mawallafi : Suleiman Babayo
Edita : Saleh Umar Saleh