Tashar DW ta nuna bacin ranta ga Najeriya bisa tsare wakilinta na Kaduna | Labarai | DW | 25.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashar DW ta nuna bacin ranta ga Najeriya bisa tsare wakilinta na Kaduna

Kafar yada labaran ta DW ta ce ta tura wakilinta na Kaduna Ibrahima Yakubu a ranar 23 ga watan nan na Yuni domin kawo rahoto na gangamin 'yan Shi'a sai 'yan sanda suka kama shi suka kuma ci mutuncinsa.

IIbrahima Yakubu wakilin DW a Kaduna Najeriya

Ibrahima Yakubu wakilin DW a Kaduna Najeriya

Kafar yada labaran Deutsche Welle a nan Jamus a wannan rana ta Lahadi ta tura wa mahukunta a Najeriya doguwar wasikar nuna bacin ranta bayan da ta zargi 'yan sanda da cin zarafi ta hanyar duka da ma tsare wakilinta zuwa wani lokaci a kasar.

Kafar yada labaran ta DW ta ce ta tura wakilinta na Kaduna Ibrahima Yakubu a ranar 23 ga watan nan na Yuni domin kawo rahoto na gangamin da 'yan Shi'a suka shirya, sai dai jami'an 'yan sanda sun kama shi har ma da duka inda ma aka zarge shi da zama dan Shi'ar.

Har ila yau DW ta ce 'yan sandan ba su tsaya a nan ba har da lalata kayan aikin na wakilin na DW, abin da ta ce ba za a lamunta ba sakon da ke kunshe cikin wasikar da ta aika wa gwamnatin ta Najeriya.