Tashar DW ta mayar da martani a kan China | Labarai | DW | 17.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashar DW ta mayar da martani a kan China

Shugaban tashar DW Peter Limbourg,ya maryar da martanin dangane da hukuncin ɗaurin shekaru bakwai na zaman gidan yari ga Gao Yu a China.

Hukumomi shari'a na China sun yanke wa 'yar jarida mai sunan Gao Yu tsohuwar editar wata mujalar da ake kira da sunan Economics weekly.Wacce kuma ke ba da gudunmawa ga aiyyukan jarida ga DW. Peter Limbourg ya yi Allah wadai da hukuncin sannan kuma ya ƙara da cewar

'' Tashar DW za ta dakatar da tattaunawar da take yi da gidan telabijan na China na CCTV da nufin ƙula wata hulɗa a kan abin da ya shafi harkokin al' adu.''

Hukumomin na China na zargin 'yar jaridar da laifin cin amanar ƙasa ta hanyar ba da wasu bayyanai siri ga wasu 'yan jarida na ƙasashen waje. To sai dai Gao Yu mai shekaru 71 da haifuwa ta musunta zargin.