1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Venezuela na kara zafi

Gazali Abdou Tasawa
January 23, 2019

A Venezuela magoya bayan gwamnati da na 'yan adawa na gudanar kowanne daga na shi bangare da zanga-zanga a wannan Laraba a birnin Caracas domin kalubalantar manufofin juna. 

https://p.dw.com/p/3C2Ga
Venezuela Unruhen nach versuchter Meuterei
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Llano

'Yan adawar kasar ta Venezuela dai wadanda suka yi yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 20 ga watan Mayun da ya gabata wanda Shugaba Nicolas Maduro ya lashe sun kira magoya bayansu ne su fito domin neman a kafa gwamnatin rukon kwarya da kuma shirya sabbin zabuka domin maye gurbin Shugaba Maduro da suka kira shugaban kama karya kamar dai yadda Jorge Millan daya daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ta Venezuwela ya bayyana a wajen taron gangamin 'yan adawar: 

Ya ce "Doli mu kori mai da mai kwacen mulki domin hatta sojojin kasar nan sun soma fitowa suna nuna kosawarsu da wannan shugaba wanda yanzu haka yake tsare da sojoji sama da 400 a gidajen kurkuku yana gana masu azaba."

Wadannan tarukan gangami dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wasu sojojin kasar ta Venezuwela 27 suka tayar da boren nuna adawa da gwamnatin Shugaba Maduro a birnin Caracas bayan da suka fasa runbunan ajiyar makamai na wasu barikokin soji suka kwashi makamai. Shugaba Maduro dai ya zargi kasar Amirka da kitsa wannan yinkuri na neman kifar da gwamnatinsa