1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron zaman lafiya na duniya tsakanin mabiya addinai

August 20, 2019

Shugabannin addinai na duniya sun hadu a birnin Lindau da ke gabashin jihar Baveria a kasar Jamus da nufin gudanar da taro karo na farko domin lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai.

https://p.dw.com/p/3OCl0
Lindau Interreligiöses Treffen im Allgäu
Hoto: DW/C. Strack

Shugabannin addinai na duniya sun hadu a birnin Lindau da ke gabashin jihar Baveria a kasar Jamus da nufin gudanar da taro karo na farko domin lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai. Kawo yanzu wakilan addinai daga kasashe 100 sun samu halartar wannan babban taro na tsawon kwanaki hudu da za a fara a wannan Talata.

Wannan dai na zama taron addinai mafi girma a wannan shekarar ta 2019 shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier shi ya jagoranci bude shi. Tsawon kwanaki katafaren zoben katako da ake wa lakabi da "Ring of Peace" ke girke a dandalin Luitpold da ke birnin Lindau. A ta bakin Ulrich Schneider manajan daraktan gidauniyar tattaunawar zaman lafiya tsakanin mabiya addinai na duniya da kungiyoyin farar hula wanda kuma shi ne jagoran taron karo na 10, zoben na wakiltar duk wani abu da ya danganci samun daidaito da zaman lafiya.

Deutschland Lindau Konferenz Religions for Peace
Taron zaman lafiya na duniya a LindauHoto: DW/Z. Ahmed

"Alamar na nuni da cewa ku zauna tare ku yi aiki tare ku tattauna matasaloli tare da samo mafaita tare ta hanyar musayar ra'ayoyi. Idan har kuka samu tattaunawa da fahimtar juna babu wata matsala ta tashe-tahsen hankula da ka iya kunno kai. A ganina batun addini batu ne mai muhimmanci, shi ne abin da za mu tattauna a nan Lindau. Addini abu ne da ya shafe mu. Sama da kaso 80 cikin 100 na al’ummar duniya suna da addini. Wannan ya na da banbanci kan yadda abun yake a nan Jamus. Addini na taka muhimmiyar rawa. A wasu lokutan shugaban addinai kan yi ruwa da tsaki. A dangane da haka yana da matukar muhimmanci mu hadu mu tattauna batun musamman dangane da yankunan da batun addnin ke zaman wani kalubale, har ma da sauran sassan duniya baki daya."

Wolfgang Schürer
Farfesa Wolfgan SchürerHoto: DW/Z. Abbany

A nasa bangaren yayin wata hira da tashar DW Wolfgang Schürer da ke zaman shugaban wannan gidauniya da aka kafa a shekara ta 1970 wadda kuma baki dayan addinan da ake da su a fadin duniyar nan ke da rijista da ita cewa ya yi yana fatan taron ba zai zama na shan shayi da aka saba gudanarwa ba tare da amfana daga gare shi ba

"Ya danganta da yadda za mu shiga cikin wannan batu da kuma yadda za mu tunkari  batautuwan da muke son tattaunawa. Muna fatan taron zai haifar da natija mai kyau da za a dade ana mora, ba irin yadda ake gudanar da taruka a kuma watse ba tare da an samu wani ci gaba ba."

Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Jamus dai ta bayar da gagarumar gudunmawa ta makudan kudin Euro domin tabbatar da ganin wannan taron ya cimma nasara. A cewar  Schneider manajan daraktan gidauniyar tattaunawar zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, yana fatan birnin na Lindau zai kasance cibiyar gudanar da taron hadin kan addinan ta din-din-din a nan gaba.