Taron yiwa gwamnatin Lebanon kwaskwarima ya watse | Labarai | DW | 11.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron yiwa gwamnatin Lebanon kwaskwarima ya watse

An tashi baram-baran a tattaunawar da ake yi da nufin yiwa gwamnatin Lebanon canje canje, bayan da ´yan siyasa dake adawa da Syria suka yi watsi da bukatun kungiyar Hisbollah da masu mara mata baya na samun karin fada a jiya cikin gwamnati. Bayan zagaye na hudu na tattaunawar shugaban ´yan adawa na Kirstoci kuma mai dasawa da Hisbollah Michel Aoun ya fadawa manema labarai cewar ba´a cimma wani sakamako ba saboda haka an katse zaman shawarwarin ba tare da an sanya ranar da za´a sake komawa kan tebur ba. Rashin nasara shawarwarin na mako guda wanda kakakin majalisar dokoki Nabih Berri ke shugabanta, ka iya janyo tabarbarewar zaman dardar wanda ka iya jefa kasar cikin rudami.