Taron ′yan adawar Siriya a Doha | Labarai | DW | 04.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron 'yan adawar Siriya a Doha

Masu adawa da Bashar Al-Assad sun ƙuduri aniyar haɗa kai domin girka gwamnatin riƙwan ƙwarya.

'Yan adawar Siriya sun fara wani taro na kwanaki huɗu a birnin Doha.

Ana kyauttata zaton 'yan adawar su zaɓi Riad Seif, wanda ya daɗe ya na gwagwarmaya da shugaba Bashar Al-Assad a matsayin shugaban sabuwar haɗɗaɗiyar ƙungiyar da su ke bukatar girkawa.

A can ma ƙasar Jordan, wani gungun 'yan adawar Siriya na cigaba da zaman taro.

Ɓangarorin biyu, sun baiyyana burin kifar da mulkin shugaba Bashar Al-Assad, amma sun yi kira ga ƙasashen duniya su ƙara taimaka masu.

A makon da muke ciki, Sakatariyar Harakokin wajen Amurika Hilary Clinton, ta zargi 'yan adawar Siriya da rabuwar kanu ,abinda a cewar ta ke matsayin babban cikas ga yunƙurin kawo ƙarshen mulkin shugaba Al-Assad.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal