Taron warware rikicin siyasar Tunisiya
October 26, 2013Nan gaba a yau ne dai masu shiga tsakani za su hadu domin girka wani kwamiti na ƙwararru da zai fidda kundin tsarin mulkin ƙasar na wucin gadi, kwamitin da aka yi ta jan kafa wajen girkawa tun kusan shekarun biyun da suka gabata. A jiya ne dai aka buɗe wannan taro inda shugabannin jam'iyyar Ennahada da ke yin mulki a ƙasar da kuma 'yan adawa suka gudanar da wata tattaunawar da ta kai su cikin tsakar daren jiya a wani yunƙuri da suke yi na yanke shawarar irin gwamnatin da za a girka.
Gabannin fara wannan taron dai, firaministan ƙasar Ali Larayedh ya yi alƙawarin yin murabus wanda zai ba da damar naɗa wani sabon firaminista da ma girka sabuwar gwamnati sai dai kawo yanzu wasu 'yan adawar ƙasar na nuna shakku game da hakan.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane