Taron shugabannin kasashen gabashin Afrika | Labarai | DW | 20.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabannin kasashen gabashin Afrika

Shugabannin kasashen gabashin Afrika sunyi kira da a hada hannu wuri guda a kokarinsu na kawadda yunwa da fari da sukayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare kuma da sanya miloyoyin jamaar yankin cikin balain yunwa.

Shugabannin na kasashe 6 da suke ganawa yau a birnin Nairobi na kasar Kenya,suna kuma sake duba kokarin samarda zaman lafiya a kasashen Somalia da Uganda da kuma kokarin sasanta rikicin kann iyaka daya ki ci yaki cinyewa tsakanin Habasha da Eritrea.

Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki,wajen bude taron,ya roki alummomin duniya da su taimaka a yaki fashin jiragen ruwa da akeyi akan ruwayen Somalia,inda kawanaki 2 da suka shige akayi musayar wuta tsakanin jiragen yakin ruwa na Amurka guda 2 da wasu yan fashin jiragen ruwa,inda aka kashe dan fashi daya wasu 5 kuma suka samu rauni.

Yayinda kuma aka cafke da dama daga cikinsu.