Taron shugabanni a Chadi a kan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 09.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanni a Chadi a kan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Shugabannin ƙasashen yankin tsakiya na Afirka na yin taro a Chadi da nufin samar da hanyoyin kawo ƙarshen tashin hankalin da ake fama da shi a Afirka ta Tsakiyar.

Babban magatakardan na Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yankin na Tsakiyar Afirka(CEEAC). Allami Ahmet, ya ce an kira taron ne dangane da yadda al'amura suka ƙara taɓarɓarewa a ƙasar amma kuma shugabannin Bangui sun gaza yin wani yunƙuri.

Ya kuma ƙara da cewar taron ba wai zai tattauna maganar neman sauyi gwamnati ba ne ko kawo wani canji ga gwamnatin riƙon ƙwaryar. Tuni da da shugaba Michel Djotodia na Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya t ya isa a birnin N'Djamena. Jami'an ƙungiyoyin agaji dai da na hukumar UNICEF sun yi gargaɗin cewar ƙasar na daf da faɗa wa cikin wani mugun hali.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu