Taron shugabanin yankin mashigin ruwan Gini | Labarai | DW | 24.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin yankin mashigin ruwan Gini

Shugabanin ƙasashen da suka ratsa ruwan Gini na taron tabbatar da tsaro kan ruwan da ma daukan matakan yaƙi da feshin tekun da ya addabi yankin.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya na Kamaru inda shugabannin yammaci da tsakiyar Afirka ke taro a Yaounde, kan hanyoyin tabbatar da tsaro wajen harkokin sufurin ruwa da kuma dauƙar ƙwararan matakai kan fashin jirgin ruwan da ya addabi ƙasashen da ke yankin mashigin ruwan Gini.

Wannan taro, na zuwa ne daura da alƙalumar da hukumar IMB - Cibiyar da ke bincike kan fashin teku ta fitar, wadda ta nuna cewa matsalar ta yi ƙamari har ta wuce ta somaliya, kasancewar a bara kawai aƙalla matuƙan jirgin ruwa 966 aka kai wa hari

Takardun da shugabanin za su rattaɓawa hannu sun haɗa da sabbin yarjeniyoyi da kuma shiri na musamman kan yaƙi da fashin teku da sauran miyagun abubuwan da ke faruwa a kan ruwan, da ma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ƙungiyar raya tattalin arziƙin yammacin Afirka wato ECOWAS, da takwararta ECCAS wacce ke raya tattalin arziƙin ƙasashen tsakiyar Afirka tare da Hukumar tabbatar da kariya da tsaro a yankin na mashigin ruwan Gini.

Bayan an kammala wannan taro ana kuma sa ran cewa shugaba Jonathan zai gana da mai masaukin baƙi Paul Biya inda za su tattauna matsalar tsaron da ke tsakanin iyakokin ƙasashen nasu da ma yanayin jin daɗin 'yan Najeriyar da ke zaune a Kamaru.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal