1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan rikicin Burkina Faso

Usman Shehu Usman RGB
December 16, 2022

Taron shugabanin Afirka a birnin Washington da rikice-rikice a kasashen Burkina Faso da jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4L4tZ
Taron shugabanin Afirka a birnin Washington na Amirka
Taron shugabanin Afirka a birnin Washington na AmirkaHoto: Kevin Dietsch/Getty Images via AFP

Jaridar Die Tageszeitung ta fara sharhinta kamar haka. Babu karshen ta'addanci a yankin Sahel bisa ga dukkan alamu. Tallafin jin kai ya yi karanci ga mutane miliyan biyu da suka rasa matsugunansu a Burkina Faso, kuma fatan komawa kauyukansu na dakushewa a kullum. A duk fadin kasar, kusan mutane miliyan biyu ne ke gudun hijira, hakan na nufin kusan kashi goma na al'ummar kasar kenan a yanzu rikici ya raba da gidajensu.

A nata sharhin Jaridar  Der Tagesspiegel, gabanin janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, mai zai faru a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango? Der Tagesspiegelt ta ci gaba da cewa, a karshen watan Nuwamba, an kashe fararen hula 272 a wani kisan gilla da wata kungiyar 'yan tawaye ta yi a gabashin kasar. Wannan ya kara sukar tawagar Majalisar Dinkin Duniya wace aka sani da Monusco, kuma zai iya kai ga kawo karshen ta. Ko rundunar za ta iya samar da karin kwanciyar hankali a nan gaba, amma akwai shakku.

DR Kongo | MONUSCO | Unrühen
Rundunar MONUSCO a KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Sai kuma batun siyasar duniya, inda Süddeutsche Zeitung ta ce, zawarci tsakanin masu ikon fada a ji a duniya, jaridar na magana ne bisa taron shugaban Amirka Joe Biden da Afirka wanda ya kare cikin kokwanto. Shugaban Amirka ya yi niyyar bai wa bakinsa na Afirka kyauta ta hanyar tarbar shugabannin kasashe da gwamnatoci 49 zuwa taron kwanaki uku. Magabacinsa, Barack Obama, shi ne ya kirkiro da tsarin inganta alaka da nahiyar Afirka. Shugaban Amirka Ba-Amurke na farko ya yi alkawarin sabon zamanin hadin gwiwa. A cikin 2014, amma nan da nan shekaru suka yi saurin gudu kuma alkawuran na Obama sun kasance wadanda ba a cika ba. Yanzu Biden yana son farfado da burin Obama, amma kuma bisa darasin alkawuran Obama, shugabannin na Afirka na cewa mu dai gani a kasa.

Masu faffukar kare muhalli
Masu faffutukar kare muhalliHoto: John Linton/empics/picture alliance

Sai wani sharhin da jaridar Die Tageszeitung ta wallafa bisa makashi. Inda jaridar ta ce inganta kamun kifi maimakon iskar gas. Jaridar ta kara da cewa Kungiyoyin kare muhalli na kasashen Jamus da Senegal, sun yi kira ga gwamnatin da cibiyoyin bada kudi na habaka makamashi da su yi tunani. Kungiyoyin na sukar cewa, manufofin gwamnatin Jamus na sayo makamashin gas daga Senegal hakan na yin barazana ga ayyukan masunta da dama a Senegal. Kungiyar kare mahalli da aka sani da Friday for Future, wace ke da rassa a kasashen biyu, ta yi kira ga hadakar samar da makamashi da kada ta tallafa ko kuma ba da kudi ga shirin yin amfani da iskar gas a gabar tekun Atlantika na kasar Senegal.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani