Taron samar da tallafi ga yankin Darfur na Sudan | Labarai | DW | 07.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron samar da tallafi ga yankin Darfur na Sudan

A tattaunawar kwanaki biyu da aka bude a wannan Lahadi Qatar, ƙasashen duniya masu ba da tallafi, za su yi ƙoƙarin samar da kuɗaɗen sake gina Darfur.

Wakilai na ƙungiyoyi masu zaman kan su da gwamnatoci kusan 400 suka hallara a taron da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a birnin Doha na Qatar, tare da ƙasashe masu hannu da shuni domin samar da wata gidauniya don sake gina yankin Darfur na Sudan, wanda ya yi fama da yaƙin basasa sama da shekaru goma.

Taron wanda za a tattaunawa, ranakun Lahadi da Litinin, ana sa ran za a samar da sama da biliyan bakwai na kuɗaɗen karo karo domin taimaka wa yankin a tsarin ayyukan raya ƙasa na shekaru shidda. Jorg Kühnel wani jami'in hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yin ayyukan ci gaban al'umma wato PNUD ya baiyana cewar.

"Wannan tsari zai bai wa yankin Darfur ɗin, cikakken 'yanci ta yadda yankin zai bunƙasa harkokinsa na tattalin arziki da tsara hukumominsa da kuma ma'aikatu.''

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal