Taron ministocin cikin gida na EU a Brussels kan matsalar ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 10.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministocin cikin gida na EU a Brussels kan matsalar 'yan gudun hijira

Ministocin cikin gida na EU na wani taro a wannan Alhamis domin tattauna batun matsalar 'yan gudun hijira biyo bayan matakin kasar Sloveniya na rufe hanyar shiga yankin Balkan ga 'yan gudun hijira.

Taron wanda zai dauki kwanaki biyu zai nazarin sabbin shawarwarin da Turkiyya ta bayar a taron da ta gudanar da shugabannin kasashen tarayyar Turai ta EU kan batun matsalar 'yan gudun hijirar. Turkiyyar dai ta yi alkawarin daukar ilahirin bakin hauren da ke neman shiga Turai idan kasashen Turan za su zuba mata kudi tsaba har Euro biliyan shida, domin daukar nauyin 'yan gudun hijirar Siriya miliyan biyu da dubu 700 da ke zaune a cikin kasarta.

Ministocin cikin gida na kasashen EU dai za su mayar da hankali kan batun matsalar 'yan gudun hijira biyo bayan matakin da kasar Sloveniya ta dauka, inda a ranar Laraba ta rufe hanyar shiga yankin Balkan ga 'yan gudun hijira da ke ratsawa kasar zuwa sauran kasashen Turai.