Taron matasa Krista a Brazil | Siyasa | DW | 23.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron matasa Krista a Brazil

Tun daga ranar 23 ga wannan wata na Yuli zuwa 28 ake gudanar da taron matasa na duniya a Brazil wanda ke samun halartar shugaban ɗarikar Roman Katolika, Fafaroma Francis.

Matasa kusan miliyan ɗaya da rabi ne daga ƙasashen duniya kusan 170 aka shirya za su halarci wannan taro, wanda zai yi bita dangane da muhimman batuttuwan da suka shafi rayuwar yau da gobe ta matasa 'yan ɗarikar Katolika.

Cuɗanya tsakanin matasa na ƙasashe daban-daban

Galibin waɗanda ke hallartar taron sun fito ne daga yankin Latin Amirka, kuma saduwar na zuwa ne dadai lokacin da tashe-tashen hankula da ake fuskanta a ƙasar saboda abin da jama'ar suka kira tsadar rayuwa da cin hanci da karɓar rashawa da kuma kashe kuɗaɗen da ƙasar ta ke yi ta hanyar yin amfani da su cikin harkar ƙwallon ƙafa.

Amma duk da haka ana yi wa taron kallon wani abin da matasan suka zaɓu su gani domin saduwa da jagoran ɗarikar ta Katlokia wato Fafaroma Francis, wanda shi ne karo na farko da yake kai ziyara a wata ƙasa tun bayan da aka naɗa shi a kan matsayin watannin biyar da suka gabata. Taron dai zai kasance cuɗanya da kuma canza yawu tsakanin matasan ma'abiya ɗarikar na sassa daban-daban na duniya. Odom Orani wani jagoran addini ne a ƙasar ta Brazil.

Ya ce : ''Maziyarta da dama za su yi tambayoyi dangane da yadda matasa ke yin rayuwa a yankin na Latin Amirka da yadda suke fama da talauci da kuma maganar samar da ilimi a cikin makarantu.''

Fargabar samun tashin hankali a lokacin taron

Halin tafiyar hawainiya wajan samun ci-gaba a ƙasar wanda matsalolin tattalin arziki suka haifar,sun tilasta wa dubban jama'ar yin zanga-zanga domin neman sauye-sauye, Junior Walmyr ɗalibi ne da ke karanta ilimin kimiya a ƙasar ta Brazil.

Ya ce :'' za mu sanar da duniya cewar mu mabiya addinin Krista za mu iya kawo canji ga rayuwar al'umma cikin lumana ba tare da tayar a fitina ba.''

An jibge sojoji kusan dubu 22 a birnin na Rio de Janeiro domin waɗannan bukukuwa domin kiyaye afkuwar yamutsi na jama'a wanda ake da fargaban ka iya rage armashi haɗuwar daga ɓangaren ƙungiyoyin na kusa da 'yan luwadi da ke adawa da matakin da Cocin Katolika ta ɗauka,na ƙin ba da haɗin kai ga auren jinsi ɗaya. Gabannin zuwan na Fafaroma sai da aka gano wani bam da aka ɗana kafin wasu jama'ar su yi zanga-zanga. An kashe kuɗaɗe miliyan 118 na Euro saboda wannan biki.

Daga ƙasa za a iya sauraran wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin