Taron KTT da kasashen Tekun Baharrum | Siyasa | DW | 28.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron KTT da kasashen Tekun Baharrum

A jiya lahadi aka gabatar da taron koli na yini biyu tsakanin KTT da Kasashen Tekun Baharrum a Barcelona

Taron Barcelona

Taron Barcelona

Ita dai maganar yaki da ta’addanci ita ce aka sha famar kai ruwa rana kanta a zauren taron kolin da aka fara a jiya lahadi, wanda da yawa daga cikin shuagabannin kasashen musulmi dake kudancin gabar tekun Baharrum suka ki halarta. Hakan ya haifar da cikas ga shagulgulan bikin murnar samun shekaru goma da kulla wannan kawance tsakanin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai (KTT) da na kudancin gabar tekun Baharrum. A cikin jawabinsa na bude taron sarki Juan Carlos na kasar Spain ya ce wajibi ne a dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma samar da yalwa a yankin tekun Barahrum.

„Daidai da shekarar 1995 a halin da muke ciki yanzun ma muna iya batu a game da shiga wani sabon babi na dangantaka tsakanin dukkan kasashen dake halartar zauren taron nan. Kuma alakarmu tana tattare da kyakkyawar makoma.“

Shekaru goma bayan gabatar da wannan manufa ta kawance tsakanin kasashen Turai da na kudancin gabar tekun Baharrum, har yau wannan dangantaka tana da muhimmanci, in ji sarki Carlos.

To sai dai a bayan fage ba a mayar da hankali ga shagulgula ba. Wakilai 35 dake halartar taron sun dukufa ne akan maganar demokradiyya da kare hakkin dan-Adam da kuma matakan yaki da ta’addanci. Kasashen KTT na bukatar ganin kawayensu Larabawa sun dauki karin matakai na garambawul da girmama hakkin dan-Adam. Ta haka kasashen na larabawa zasu samu karin taimakon tattalin arziki da misalin kashi 15% a matsayin tukwici ga duk kasar da ta bi wannan manufa. Karamin minista Abdelaziz Belkhadem na kasar Aljeriya yayi fatali da abin da ya kira wai neman yi wa kasarsa shisshigi a al’amuranta na cikin gida daga bangaren kasashen KTT. Ya ce kasar ba zata yarda da duk wata manufa ta matsin lamba saboda kwadayin samun wani dan taimakon kudi. Shi kansa shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika bai samu halartar taron ba, ya zarce ne zuwa birnin Paris domin neman magani. Shugaban ya bi saun sauran shuagabannin kasashen Larabawa da suka ki halartar taron, in banda shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas. Wasu bayani sun ce shuagabannin na kasashen Larabawa sun ki halartar taron ne saboda wasu tsauraran shuruddan da a ganinsu kasashen Turai na neman wuce gona da iri ne wajen shimfida su. Daya sabanin da ake fama da shi tsakanin sassan biyu kuma shi ne game da matakan murkushe ta’addanci da kuma ainifin fassarar da za a ba wa kalmar ta’addancin. Misali da yawa daga kasashen Turai na bukatar ganin taron yayi Allah Waddai da hare-haren dakarun Palasdinawa akan Isra’ila, wadda ke da wakilci a gamayyar ta kasashen Turai da na kudancin gabar tekun Baharrum, a yayinda su kuma Larabawa a ganinsu wanannan hare-hare hakki ne na Palasdinawa a fafutukar neman ‚yancin kansu.