Taron koli ya duba matsayin Turai kan 'yan gudun hijira
October 25, 2013A kowace rana, ƙananan jiragen ruwa ɗauke da 'yan gudun hijira ke shiga ƙasar Italiya, kuma wannan ta zama masu babbar matsala. A dalilin haka ne mahukuntan Italiya suka yanke shawarar cewa wajibi ne ƙasashen Turai baki ɗaya su raba alhakin ɗaukan 'yan gudun hijiran, sai dai duk da haka, banda batun tsaron iyakokin ƙasashen Turai da tabbatar lafiyar 'yan gudun hijiran, yawancin wakilan ƙasashen da suka kasance a taron ƙolin Ƙungiyar Tarayyar Turai na wannan karon ba su bada wata gudunmawa wajen shawo kan wannan matsala ba.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron ƙolin na Ƙungiyar Tarayyar Turan da ya gudana a birnin Brussels yau har da magajin garin Lampedusa na ƙasar Italiya Guisi Nicolini, wadda ta zo ta gabatar da ƙorafinta ga shugabanin gwamnatocin nahiyar, domin samun goyon bayansu.
Tanadin dokokin Turai kan karɓar baƙi
Gwamnatin Italiya na ganin nauyin ya yi mata yawa na kula da 'yan gudun hijiran da ke shiga ƙasar a kowace rana ta Allah, kuma a ganinta kamata yayi suma sauran ƙasashen su raba wannan nauyi. Firaministan Italiya Enrico Letta wanda ya tabbatar wannan batu ya kasance kan gaba a taron ya ce suna buƙatar mataki mai ƙwari
"A gani na, tilas ne mu ɗauki mataki na bai ɗaya a matsayinmu na Turai, kuma daga abin da na gani yau, a ra'ayi na matakin da aka ɗauka mai ma'ana ne, yanzu mun san cewa Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ɗauki wannan batu da mahimmanci, kuma a gani na matakin da aka dauka na da mahimmanci"
Sai dai bisa tanadin dokokin Turai, duk wani ɗan gudun hijira, zai iya samun takardar izinin zama ko kuma mafaka ne a ƙasar Turan da ya fara taka ƙafa, saboda haka, duk ɗan gudun hijirar da ya shiga Turai ta Italiya misali, sai kuma daga nan ya tafi Jamus, jami'an kan iyakar Jamus zasu iya tasa ƙeyarsa zuwa Italiya tunda nan ya fara sanya ƙafa, amma a waje guda kuma, shugabanin na ganin cewa ko da shi ke matsala ce da ta shafi nahiyar baki ɗaya, ƙasashensu ba su da ƙarfin karɓar yawan mutanen da ke shigowa nahiyar.
Hana gudun hijirar tun farko
Yawancinsu, a ɓoye ma suna farin cikin kasancewar irin wannan doka, domin 'yan gudun hijira ƙalilan kaɗai suke so su ɗauka, hasali ma gara musu idan ma tun farko basu baro ƙasashensu na ainihi ba. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nunar da cewa ya kamata a tabbatar da tsaro kan iyakokin dan kare hatsari daga afkuwa
" Akwai mahimmancin gaske a ce an sami haɗin kai wajen tabbatar da tsaron 'yan gudun hijirar daga ƙasar da suke fitowa, zuwa ƙasar da suke shiga. Batun ƙarfafa hukumar tsaron iyakoki na Frontex ya taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawar da aka yi domin babu shakka suna ƙoƙarin yaƙi da miyagun ayyuka amma kuma mun san cewa wannan aikin yana tattare da sarƙaƙiya"
Fargabar samun matsalar cunkoso
A duk cikin shugabanin, shugaba Francois Hollande na Faransa kaɗai ya fito kai tsaye ya bayyana zuciyarsa yana mai cewa:
"Mene ne aikinmu? alhakinmu ne mu tabbatar cewa waɗannan mutanen sun sami kyakyawar makoma a ƙasashensu na asali. Ba wai bayar da mafaka ga duk waɗanda suka ƙetara suka zo Tuari ba ne abin da ya dace, wannan tamkar mafarki ne, zaku iya tunanin irin matsin lambar da wannan zai janyo, idan kuka yi la'akari da irin abubuwan da wasu ƙasashenmu ke fiskanta yanzu"
Ko a sauran ƙasashen Turan, akwai ƙaruwar adawa da shigowar baƙi saboda haka, shugabanin na ganin cewa kaɗan nai zai sauya a dokokin da suka shafi siyasar 'yan gudun hijira. Yawancinsu na takaicin hatsarin jirgin ruwan da yayi sanadiyyar rayukan 'yan gudun hijira a kwanakin baya amma matakin da suke ganin ya dace a ɗauka shine tabbatar da tsaron waɗannan 'yan gudun hijira.
Mawallafa: Hasselbach Christoph/ Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu