1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron karfafa huldar kasashen Afirka da Asiya

Muntaqa AhiwaApril 21, 2015

Shugabannin kasashen Afirka da na Asiya sun hadu a kasar Indonesiya don tunawa da nasarorin da huldar kasashen ya cimma a shekaru 60 da suka gabata, kana a inganta huldodin arziki.

https://p.dw.com/p/1DGJ3
Afrika Gipfel in Tokio Shinzo Abe Hailemariam Desalegn
Hoto: STR/Afp/Getty Images

Sai dai manazartan harkokin duniya na hasashen cewa, taron da ake ganin na bunkasa harkokin kasashen ne, yana iya komawa wani batu na nuna karfi, wanda ka iya shafe duk wani ikirari na hadin kan kasashen.

Taron wanda shugaba Xi Jinping na kasar China da Firaministan kasar Japan Shinzo Abe da shugaba Hassan Rouhanin na kasar Iran dama shugabannin Afirka da dama suka halarta. za a yi shi ne sabo da tunawa da ginshikin da aka kafa na kasashe 'yan ba-ruwan-mu a zamanin yakin cacar baka tsakanin manyan kasashen duniya da Rasha, zaman da aka yi irinsa a shekara ta 1955.

Wasu daga cikin kasashen da shugabanninsu ke wakiltansu a wannan taron irinsu China da Japan, a yanzu sun kasance cikin masu karfin tattalin arziki a duniya. Manazartan dai na ganin kasashe 80 na nahiyoyin biyu, da ke taron na yini biyar, da wuya su cimma abin tasiri saboda dalilai da ba za a iya raba su da son zuciya ba.

Sai dai fa duk da wannan hasashen, shugaba Joko Widodo na Indonesiya mai masaukin baki, ya ce ba haka abin ya ke ba.

"Ya ce na yi imanin wannan taron, dama ce muka samu ta yadda za mu hada kai don bunkasa harkokinmu na zuba jari, saboda ci-gaban mu baki daya. Hadin kan namu zai taimaka wa masu tasowa daga cikinmu, ga kuma kara dankon zumunci a tsakanin nahiyoyin na mu baki daya. Tilas mu kara himma ga cinikayya tsakaninmu. Tilas mu samar da tsare-tsare masu fa'idar gina tattalin arziki, tare da samar da hanyoyin kyautata hada-hada tsakanin nahiyoyinmu. Duk wadannan matakan da na zayyana, tilas mu yi su cikin tsanaki tare da la'akari da sharudan cinikayya na kasashen duniya"

Wasu daga cikin shugabannin kasashen nahiyar Afirka da suka halarci taron, sun bayyana nufin samun nasarorin da za su taimaka, wajen habaka karfin arzikin kasashensu da ke fama da kwan gaba- kwan baya.

Mataimakain shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya yi jawabi lokacin bude taron, inda ya nuna bukatar kasashen nahiyoyin Afirka da na Asiyan, su yi kokarin cike gibin dake tsakaninsu.

"Muna bukatar karfafa kasuwanci tsakanin Afirka da Asiya, domin tabbatar da ganin mun cimma burin bunkasa arzikinmu. Muna kuma da bukatar magance irin gibi da ke a halin yanzu tsakanin duk wasu huldodi na kasuwancin nahiyoyin namu. Ta hanyar karfafa hadin kan, zamu bude sabon babin cinikayya a duniyar yau, wanda zai karfafa mu a nahiyoyin nan na duniya biyu, da ke habaka cikin hanzari. Lallai yin hakan zai hada kanmu wajen cimma buri a dukkanin matakan arziki"

Bayan wannan taron dai, ana sa ran shirya wata ganawa tsakanin shugabannin kasashen, za kuma su yi zaman yini biyu. Inda shugabannin kasashen China da Japan da Zimbabwe dama wasu shugabannin kudu maso gabashin Asiya, za su halarta.

Indien Einfluss in Afrika India-Africa Forum Summit
Hoto: Getty Images
Xi Jinping Afrikareise
Hoto: picture-alliance/dpa