Taron kafofin yada labarun duniya da DW ke shiryawa | Labarai | DW | 30.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kafofin yada labarun duniya da DW ke shiryawa

Taken taron na bana da ke zama karo na bakwai shi ne kan yada labaru zuwa shiga a dama da ku-kalubale ga kafofin yada labaru.

A safiyar wannan Litinin shugaban tashar Deutsche Welle Peter Limbourg ya yi jawabin bude babban taron kafofin yada labarun duniya na Global Media Forum, wanda Deutsche Welle ke daukar nauyin gudanarwa a kowace shekara. A jawabin na sa Limbourg ya yi maraba da baki kimanin 2000 da ke halartar taron daga kasashen duniya kusan 100. Taken taron na bana karo na bakwai shi ne "daga yada labaru zuwa shiga a dama da ku-kalubale ga kafofin yada labaru", kamar yadda Limbourg ya yi karin haske yana mai cewa: "taron na samun halarcin mutane daga bangarorin kafofin yada labaru, 'yan siyasa, 'yan kasuwa da kuma masu ilimin jami'a. Za su tattauna don samun bayani ga kalubalen da duniya ke fuskanta na ci gaba, da kalubale da kafofin yada labaru ke taka muhimmiyar rawa a ciki."

Za a dai kwashe kwanaki uku ana gudanar da wannan taro a cibiyar taruka ta duniya wato World Conference Center da ke daura da tashar Deutsche Welle.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar