Taron kafafen yada labaru na Global Media Forum na 2017 | BATUTUWA | DW | 19.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Taron kafafen yada labaru na Global Media Forum na 2017

An bude babban taron 'yan jaridu da kafafen yada labaru na duniya 'Global Media Forum' da tashar DW ke shiryawa a kowace shekara. Taron da shi ne irinsa karo na 10, ya sami halartar wakilai 2000 daga kasashe 130.

Wadannan wakilai 2000 da tashar ta DW ta gayyato za su kwashe kwanaki uku suna tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi 'yancin fadar albarkacin baki da siyasa da al'adu da batutuwan da suka shafi ta'addanci gami da tashe-tashen hankula da ake fuskanta a wurare daban-daban wanda dukanninsu batutuwa ne da kafofin yada labarai ke kawo ta su gudunmmawa a kan su. Duk da cewa taro ne da ya zama al'ada ga tashar ta DW, wasu abubuwan da ake dubawa sun shafi makoma. Peter Limbourg shi ne babban daraktan tashar DW mai watsa shirye-shirye zuwa sassan duniya cikin harsunan kasashen duniya 30.

Peter Limbourg, shugaban tashar DW

Peter Limbourg, shugaban tashar DW

"Ba mu karkatar da idanunmu kan abubuwan da suka gabata, sannan muna mayar da hankali kan wasu ma da ke zuwa nan gaba. Kuma ina tsammanin a wannan karo, batun kirkirar fasa'o'i na zamani shi ne batun da zai dauki hankalin taron na 'yan jaridun daga kafafen watsa labaru na duniya da DW ta shirya"

Da yake magana kan wannan batu Patrick Leuschdaya daga cikin manyan masu tsara wannan taro, ya ce taken taron ba wai yana nufin shi ne batun da zai mamaye taron kadai ba, amma kuma zai kasance tamkar wata gada da za a iya duba sauran batutuwan da za a tattauna lokacin taron.

"Yaya aikin ‘yan jarida ya ke a wannan lokaci na na'urorin sadarwa na zamani? Aikin jarida ya shiga cikin wani yanayi inda kowa ya kasance shi ma mai yadawa ne, kuma mai sauraro, don haka babbar ayar tambaya a nan ita ce, ta yaya aikin na jarida zai rike kimarsa?”

Al Qiblar Taron

Batun kima da mutuncin aikin jarida, shi ne babban batu da wannan zaman zai tattauna a kai ganin yadda ake samun yada labarai na karya wanda hakan ya zame tamkar ado, inda wasu ke yada bayanai marasa tushe ta kafofin sada zumunta. Kuma haka akwai battuwa akalla 40 da gungu-gungu na mahalarta taron zai tattauna a kan su. Faruk Dalhatu shi ne Daraktan Rediyon kasa da kasa na Dandal Kura da ke Maiduguri a Najeriya, wanda ke halartar wannan taro, ya dubi wannan kalubale.

Wakilai daga sassan duniya za su yi musayar bayanai da fasahohi dangane da yadda abubuwan da ake tattaunawa a kansu ke gudana a kasashensu da kuma hanyoyin da za a bi wajen kyautata su, wanda a cewar Etienne Fakaba Sisseko, Daraktan cibiyar binciken kimiyyar siyasa da tattalin arziki a Mali, da a karo na farko kenan ya halarci taron, ya ce wannan ganawar babbar dama ce a garesu.

Daga cikin wasu muhimman abubuwa masu mahimmanci da taron ya tsara, har da bada kyauta ta 'yanci da taron na DW ke bayarwa, inda a wannan karon aka bai wa kungiyar wakilan da ke aiki a fadar shugaban Amirka, ganin cewa tun bayan da ya hau karagar mulki, shugaba Donald Trump ke ta caccakar 'yan jaridu, wanda abu ne da ba za a yarda da shi ba a cewar shugaban DW. Wani abin kuma shi ne, bayar da wannan a kyauta wani mataki ne na aike wa da sako daga nan Turai zuwa kasar ta Amirka musamman ma shugabanta da ke furta kalamai marar dadi kan 'yan jarida. A ranar Laraba ce dai za a rufe wannan taron mai muhimmanci ga a kokari na inganta aikin jarida da tashar ta DW ke daukar nauyin shirya shi.

 

Sauti da bidiyo akan labarin