Taron Gwamnonin arewacin Najeriya kan tsaron yankin
December 19, 2015Talla
A yayin taron shugaban kungiyar gwamnonin arewacin kasar 19 Alhaji Kassim Shettima kana gwamnan Jihar Borno ya yi nuni da cewar:
Za su duba alamarin da ya faru ta yadda hakan ba zai ba da kofar haifar da wani abu ba ga kowaye ko kuma kungiya wajen haddasa yamutsi a kowanne lungu da sako a yankin ba. Muna fama da matsalar Boko Haram da muke kokarin magance ta.
Tun da farko mai masaukin bakin Gwmanan jihar Kaduna Malam Nasir al- Rufa'i ya yi nuni da cewar sun hadu ne bisa yamutsin yan shi'a da sojojin Najeriya a inda za su dauki matakan da suka dace don kaucewa gaba.