Taron gaggawa kan rikicin Siriya | Labarai | DW | 25.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron gaggawa kan rikicin Siriya

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani taron gaggawa a wannan Lahadi domin tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar Siriya wadda ke fama da yakin basasa.

Sakamakon yadda dakarun gwamnatin Siriya da ke samun goyon bayan sojojin Rasha ke yin ruwan bama -bamai a Aleppo inda kawo yanzu kungiyoyin farar hula da ke saka ido a Siriyar suka ce farar hula 45 suka mutu, kasashen Amirka da Birtaniya da Faransa suka ce ya kamata a kira taron domin matsa kaimi ga Rasha da ta amince a cimma shirin tsagaita wuta. A farkon wannan wata ne Amirka da Rashar suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriyar amma kuma ta wargaje mako guda bayan kai hari kan wani ayarin agaji na motocin Majalisar Dinkin Duniya.