Taron Eu kan kasafin kudi na shekaru 2014-2020 | Labarai | DW | 13.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Eu kan kasafin kudi na shekaru 2014-2020

An samu cikas a tattaunawa da ministocin kuɗi na ƙungiyar tarayyar Turai suke yi a kan kasafin kuɗi

Hakan kuwa ya biyo bayan da wakilan majalisar dokoki na ƙungiyar suka janye daga taron, abin da bisa ga dukkan alamu ake ganin zai ƙara janyo wata sabuwar dambarwa gabanin babban taron shugabannin ƙasashen Turai da za a yi kan kasafin shekarun 2014 zuwa 2020.

Shugaban majalisar Martin Schulz ya ce majalisar ba za ta halarci taron ba, kuma ya ɗora alhakin saɓanin da ake samu tsakanin ƙasashen wajan amincewa da kasafin ga shugabannin ƙasashen na ƙungiyar. An dai samu cikas ne akan tattaunawar dangane da cike wani giɓi na kusan biliyan dubu tara na Euro domin biyan wasu tsare tsare a ciki hada kuɗaɗen alahuse na ɗalibai da kuma wasu kuɗaɗen tallafi da za a baiwa Italiya saboda girgizar ƙasar da ta samu a cikin watan Mayon da ya wuce wanda ƙasahen Jamus da Faransa, da Danmark suka ƙi bada goyon baya.

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal