Taron ECOWAS akan rikicin arewacin Mali | Siyasa | DW | 11.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ECOWAS akan rikicin arewacin Mali

Shugabannin ƙasashen yammacin Afrika sun kamala wani taro a Abuja tare da amincewa da wani rahoton da ya tanadi buɗe sulhu da kuma kai soja 3,500 zuwa Mali.

Sun dai ɗauki sama da watanni bakwai su na kartar ƙasa dama barazana ga 'yan tawayen arewacin ƙasar ta Mali to sai dai kuma har ya zuwa yanzu su na taka-tsantsan ga ƙoƙarin tunkarar rikicin da ya kai ga rabuwar ƙasar gida biyu ya kuma bada damar inganta ayyukan ƙungiyar Al-Qaida da ƙawayenta a yankin.

Sama da shugabnnin ƙasashen yankin na yammacin Afrika bakwai ne da kuma wakilai daga ciki da wajen nahiyar su ka zauna a Abuja su ka ce sun amince da wani shirin maida zaman lafiya da haɗe ƙasar Mali wuri guda, shirin kuma da ya tanadi sulhu sannan kuma da amfani da karfin tuwo da nufin ganin bayan 'yan tawayen in ta kama.

Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit

Taron ECOWAS a Abuja

Sama da soja 3500 ne daga sassa daban-daban na nahiyar Afrika ne dai ake sa ran za su goya baya ga wasu soji 5000 na ƙasar Mali domin tilsata sa ke haɗe ƙasar a cewar Dr. Nuraddeen Mohammed da ke zaman ƙaramin ministan harkokin wajen tarrayar Najeriya kuma jigo a ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar ta Mali.

Ana dai kallon ɗaukacin sojojin 8,500 a matsayin abun da bai isa tunkarar arewacin na Mali da girmanta ya kai ita kanta tarrayar Nijeriya kuma ke cike da hamadar sahara da kuma yanayi marasa kyau.

Baya ga haka kuma, akwai matsala ta rashin isassun kuɗi da kayan yakin da yankin ke fatan samu daga ƙasa da ƙasa amma kuma ke fuskantar jan ƙafa da ma rashin alkawari.

Ambassada Saeed Jinnit dai na zaman babban wakilin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke da alhakin ƙarshe game da shirin yaƙin. To sai dai daga dukkan alamu hankali majalisar ya karkata ga batun sulhu da 'yan tawayen maimakon fito na fito ta hanyar yaƙi.

'Yana da matukar muhimanci a lura da sabon yunkurin 'yan tawayen malin na sulhu da gwamnatin rikon kwaryar ƙasar. Godiya ga ƙokarin tattaunawar Ecowas da kuma rawar ƙasashe irin su Algeria. Amma yana da muhimmanci wadannan kungiyoyi su tsaya kan alkawarin su sannan kuma su daina take hakkin bil adama a yankunan dake hannunsu'.

Mali Bamako Demonstration Pro Militäreinsatz

Gangamin adawa a Mali

A farkon makon jiya ne dai babbar ƙungiyar Ansar-Dine mai jagorantar ƙawancen 'yan tawayen na Mali ta nemi buɗe tattaunawar tare da aika wakilanta zuwa ƙasashen na Algeria da Burkina Faso.

Matakin kuma da daga dukkan alamu ya raba kan 'ya'yan ƙungiyar a tsakanin ƙasashe irin su Burkina Faso da kuma Ivory Cost da ke kan gaba a ƙoƙarin fifita batun na tattaunawa da kuma Nigeria da hankalin ta ke kan batun na ƙarfin tuwon da a cewar shugaban ta Goodluck Jonathan bai saɓa kudurin Majalisar Ɗinkin Duniya ba.

'Wannan na cikin tsarin ƙudurin kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya nemi amfani da ƙarfin hatsi wajen ganin bayan 'yan ta'addan da su ka maida wani ɓangare na ƙasar wani wurin da babu doka a cikin sa. Dole ne mu yi haka don kaucewa annobar da bamu son gani ba a Mali da ma nahiyar Africa da duniya baki ɗaya'.

Tarrayar Nijeriyar ce dai ake tsammani za ta bada kaso mafi tsoka na soja da kayan yaƙin da zarar shirin ya samu amincewar kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin