Taron dangi don ceto kasar Mali | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Taron dangi don ceto kasar Mali

Shugabanni a Jamus sun baiyana shirin su na taimakawa yunkurin kawo karshen tashin hankali a kasar Mali

African Union Chief Nkosazana Dlamini-Zuma (front L) and Mali's President Dioncounda Traore attend a high level international meeting in Bamako, October 19, 2012. Regional leaders joined international organisations in Bamako on Friday trying to narrow their differences over whether al Qaeda-linked Islamists in the north of Mali should be dislodged via military intervention or a more gradual political approach. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: POLITICS)

Mali Bamako Treffen Oktober 2012

Jaridun na Jamus a wannan mako sun maida hankalin su kusan gaba daya kan halin da ake ciki a Mali, musamman shirin gwamnatin Jamus na bada gudummuwa ga duk wani mataki na kawo karshen rikicin yan tawayen da suka mamaye arewacin kasar ta Mali.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace ministan taimakon raya kasashen ketare, Dirk Niebel ya baiyana goyon bayansa game da amfani da sojojin Jamus cikin rundunar da zata taimaka domin tabbatar da zaman lafiya a Mali da awo karshen mamayewar da yan tawaye suka yiwa arewacin wnanan kasa. Mali, inji Niebel, ta zama kasar dake kan hanyar rushewar ta a yanzu, inda ta wannan fuska, bata banbanta da kasashe na kusa da ita ba, kamar Guinea Bissau ko Somalia. Idan har aka shigar da sojojin Jamus a rundunar da zata kasance karkashin kulawar majalisar dinkin duniya da kungiyar hade kan Afirka, babban aikin da zasu yi shine su fahimtar da sojojin Mali kan yadda ake amfani da makamai da sauran kayan tsaro, yadda zasu iya kare kasarsu da kansu.

Entwicklungsminister Dirk Niebel (FDP, r) wird am Donnerstag (09.08.2012) in Bamako, Mali, vom malischen Übergangspräsidenten Dioncounda Traoré (M) begrüßt. Bei den Gesprächen in der Hauptstadt ging es um eine Lösung des Konflikts in dem westafrikanischen Krisenstaat. An diesem Freitag läuft ein Ultimatum ab, bis zu dem die malische Übergangsregierung konkrete Pläne und einen Fahrplan zur schnellen Bildung einer «Regierung der nationalen Einheit» vorlegen soll. Foto: Jörg Blank dpa

Dirk Niebel in Mali

Ita ma jaridar Tagesspiegel ta duba kasar Mali ne inda ta fara da cewar fataucin miyagun magun guna da yaduwar makamai da tsarin shari'a sune yanzu al'amuran da suka mamaye kasar. Mali, da ta taba kasancewar abin misali na zaman lafiya ga kasashen yamma, tun cikin watan Maris ta kasance cikin hali na rashin kwanciyar hankali. Bayan juyin mulkin da ya kayar da shugaban kasa Amadou Toumani Toure, sojojin da suka rage a kasar ta Mali sun kasa tsare ta daga yan tawayen MNLA dauke da manyan makamai da suka samu daga Libya wadanda suka mamaye arewa, suka kafawa kansu kasar da suka sdanya mata suna Azawad. Abin da ya biyo baya kuwa shine rashin tsaro da yaduwar makamai da fataucin miyagun magunguna da kujmja kafa tsarin shari'a a yankunan da yan tawayen suka mamaye.

Jaridar Die Welt tayi sharhi game da hukuncin da aka yankewa yan fashin jiragen ruwa na kasar Somaliya da aka kama, aka kuma gurfanar dasu gaban kotu a Hamburg nan Jamus. Jaridar tace wannan shari'a na yan fashin teku, shine na farko da aka yi a Jamus, tun bayan zamanin jahiliyya. An dauki tsawon fiye da shekaru biyu ana yiwa yan fashin na Somaliya shari'a, inda aka yankewa wadanda ake tuhuma dauri tsakanin shekaru biyu zuwa shekaru bakwai a gidan kaso. Jaridar Die Welt tace lokacin shari'ar kamar dai duniyoyi biyu ne suka ci karo da juna. Lauyan da ya kare yan fashin yace guda daya ne kawai cikinsu ya fahimci abin da ake yi ma gaba daya. Barayin an kama sune a shekara ta 2010, yayin da suke kokarin shiga wani jirgin ruwan daukar kaya a gabar tekun kasar ta Somaliya.

Die Angeklagten im Prozess gegen mutmaßliche somalische Piraten und ihre Anwälte sitzen am 19.10.2012 in Hamburg in einem Verhandlungssaal des Landgerichts. Foto: Philipp Guelland

Hamburg Piraten-Prozess Somalia

A wani sharhin kuma, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta tabo zaben da aka yiwa kasar Ruwanda a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. Tace zaben ta da aka yi, ya samune duk da zargin Ruwanda din da aka yi da goyon baya da taimakawa yan tawayen gabashin Kongo na M23. Karbar Ruwanda a matsayin wakiliya ta shekaru biyu a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, abune dake shan suka da rashin amincewa a duniya baki daya, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, saboda tun kafin a zabenta, akwai wani rahoto na majalisar dinkin duniya dake nuna cewar Ruwanda din tana da hannu kai tsaye a yakin basasar makwabciyarta, jamhuriyar democradiyar Kongo. A matsayin wakiliya, kasar ta Ruwanda yanzu dai tana iya kawo bata lokaci a duk wani kokari da za'a yi domin nazarin rahoton na majalisar dinkin duniya a kwamitin sulhu.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mouhamadou Awal