Taron Commonwealth cikin rarrabuwar kawuna
November 15, 2013Nan gaba kaɗan ake shirin buɗe taron ƙasashe rainon Ingila wato Commonwealth a birnin Colombo na ƙasar Siri Lanka. Taron wanda ke cike da cece-ku -ce dangane da zargin da ake yiwa hukumomin ƙasar da aikata ta'addi da kuma cin zarafin bil adama, a lokacin yaƙin da gwamnatin ta yi da 'yan tawayen Tamouls.
Shugabannin da dama na ƙasashen duniyar manba a cikin ƙungiyar sun ce ba zasu halarci taron ba, a cikin har da fira minista Kanada Stephen Harper da kuma takwaransa na Indiya Manmohan Singh. Tuni dai da aka ba da rahoton cewar firaminstan Ingila David Cameron ya isa a birni Colombo. A ƙarshen yaƙin da gwamnatin ta Siri Lanka ta kawo da 'yan ƙungiyar ta Tamouls wanda ta murkushesu a shekarun 2009. MDD ta ce mutane kusan dubu ɗari suka mutu. To sai dai hukumomin na Siri Lannka na musaunta zargin cewar sun yi ba daidai ba a lokacin yaƙin.
Mawallafi : Abdourhamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu