Taron bunkasa tattalin arzikin Masar | Labarai | DW | 13.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron bunkasa tattalin arzikin Masar

Manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa na duniya na can na gudanar da wani taro a na yini uku a garin Sharm El-Sheikh na kasar Masar.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi

Shugaban kasar Abdel Fattah al-Sisi dai na fatan taron zai taimaka wajen samun masu zuba jari na gida da na kasashen ketare a kasar. Rahotanni sun nunar da cewa tuni sakataren harkokin waje na Amirka John Kerry ya isa garin na Sharm El-Sheikh inda daruruwan 'yan kasuwa da sauran masu fada aji a duniya za su duba yiwuwar komawa huldar zuba jari da kasar ta Masar bayan tsahon shekaru hudu na tashin hankalin da take fuskanta. Sa'oi kalilan gabanin fara taron ma dai, sai da wasu kananan bama-bamai uku suka tashi yayin da wasu rokoki da aka harba a garin Sinai suka raunata sojojin kasar uku.