Taron a kan batun ′yan ci rani a Bangkok | Labarai | DW | 29.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron a kan batun 'yan ci rani a Bangkok

Ministocin harkokin waje daga ƙasashe 17 na Asiya za su tattauna yadda za a shawo kan matsalar 'yan ci rani.

Taron zai fi mayar da hankali ne a game da yadda za a shawo kan matsalar kwarar baƙin haure daga yankin Asiya ta Kudu ta ɓarauniyar hanya ta ruwan teku.

Wadanda ke tserewa daga ƙasashen Myanmar da Bangladesh zuwa Malaysia da Indunusiya.Sama da baƙin haure dubu ukku ne dai na ƙasashen Myanmar da Bangladesh waɗanda suka kwashe dogon lokaci a kan ruwan teku suna yawo suka samu mafukar a ƙasashen Malaysia da Indunisiya da kuma Tailand a yan kwanakin nan.