Taron ƙasashe renon Ingila a Sri Lanka
November 16, 2013Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin an gudanar da bincike mai zaman kan shi kan zarge-zargen aikata manyan laifukan yaƙi a ƙarshen yaƙin basasar ƙasar Sri Lanka, wanda ya ɗauki tsawon shekaru 26, abin da kuma ya fusata shugaban ƙasar Sirilankar Mahinda Rajapaksa, inda aka rawaito shi yana cewa duk mai ruwa kada ya zagi kada, bayan da Mr Cameron ya ce ya kamata ƙasar ita ma ta gudanar da nata binciken kafin watan Maris na shekara ta 2014 ko kuma ta fiskanci tuhuma daga kwamitin ƙasa da ƙasa.
Firaministan Birtaniyan David Cameron ne ya gota kowa wajen yin suka ga yanayin da ake tafiyar da harkokin kare hakkin bil adaman ƙasar, a taron Commonwealth ko kuma ƙasashe renon Ingilan dake gudana a Colombo babban birnin ƙasar.
Dakarun Sri Lankan dai sun murƙushe 'yan awaren Tamil Tigers a dagan ƙarshe na yaƙin da aka yi a shekara ta 2009 a wata maƙarƙashiyar da ake zargin ɗan uwan shugaba Rajapaksa, wato Gotabaya Rajapaksa da ƙullawa lokacin yana riƙe da muƙamin ministan tsaro.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh