Taro kan tura Sojoji arewacin Mali | Siyasa | DW | 30.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taro kan tura Sojoji arewacin Mali

Gamayyar Afrika ce ke jagorantar taron na Bamako dangane da tsara shirin tura sojoji yankin arewacin ƙasar Mali, bisa ga cikar wa'adin Majalisar Ɗunkin Duniya.

Arewacin Mali dai ya kasance yanki ne na sahara tsantsa, wanda bisa la'akari da Yadda yanayin wurin yake, zai kasance abu mawuyaci wa sojojin da basu da horo na musamman kan faɗa yankin sahara su iya tabuka komai. Sojojin ƙasar Tchadi dai suna da masaniya dangane da wannan yanayi. adangane da hakane ma tun lokacin da aka fara tattauna batun amfani da sojoji wa yankin arewacin Mali, ake mahawara kan sojojin na Tchadi.

Sai sai akwai ayar tambaya dangane da ko Chadin zata iya kasancewa abar dogaro dangane da samar da zaman lafiya a yankin Sahel. Ta dai kasance wata da itama ba za'a iya cewar akwai zaunanniyar zaman lafiya ba. Shugaba Idris Deby Itino ya yiwa ƙasar kamun kazar kuku tun tsawon shekaru 20 da suka gabata, ko kaɗan baya wasa da 'yan adawa, kuma yana da rundunar sojoji kakkarfa dake tsare gwamnatinsa.

Mali Demonstration Demonstrant Transparent Menschen Gruppe Bamako

Gangamin adawa

Shugaba Deby dai ya hana 'yan adawa yin sakat a ƙasar, balle basu damar tofa albarkacin bakinsu kan lamuran kasa. A watan satumban daya gabata nedai aka haramta wata maujalla, sakamakon wallafa wani labari datayi kan cin hanci da karɓar rashawa a wannan ƙasa. Tuni dai aka jefa Editan mujallar a kurkuku, kazalika marubata labaran kuma 'yan kwadago su uku. Adadin mutanen da ake ci gaba da cin zarafinsu ta hanyar kame dai bashi da iyaka a cewar Christian Mukosa na kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty, daya jima yana lura da al'amuran a ƙasar ta Tchadi.

Ya ce " a watan oktoba nan ne aka tilastawa wani Bishop na roman katolika barin ƙasar, saboda a yayin jawabinsa ga taron masu ibada, ya bayyana cewar babu adalci a rabon kuɗaɗen albarkatun man Tschadi tsakanin al'ummomin wannan ƙasa. Kuma wannan shine karon farko da aka kori wani bishop daga wannan ƙasa".

Gwamnatin ƙasar ta Tchadi na cin zarafin al'umma ba tare da wata rufa- rufa ba acewar christian Mukosa. Domin ko Alkalan ƙasar ma basu da ta cewa kan wannan hali.....

Ya ce" amfani da kotunan shari'a da wasu hukumomin aiwatar da hukunci wajen yiwa 'yan jarida da wasu masu tofa albarkacin bakinsu barazar tozartawa, wani sabon abu ne a dake da matukar damuwa. Domin a baya akan yi musu irin wannan barazana ta tsoratarwa a fakaice, amma yanzu gwamnati na amfani da sashin shari'a wajen cin zarafin 'yan adawa".

Mali Bamako Treffen Oktober 2012

Mahalarta taron Bamako

Wannan mahawara dangane da amfani da sojojin Tchadi a arewacin Mali dai nada nasaba ne da dangantar dake tsakaninta da Faransa, inda ake ganin Tchadin zata yi tasiri saboda ƙwarewar dakarunta kan faɗa a sahara. To saidai acewar masaniyar kimiyar siyasa a cibiyar Arnold-Bergstraesser da ke Freiburg Helga Dickow, akwai ayar tambaya dangane da yin amfani da sojin Tchadin a arewacin Malin duk da ƙwarewarsu a sahara.....

Ta ce " wane irin kwatancin demokraɗiyya muke nunarwa a yammaci, idan kwai zamu bukaci goyon bayan ƙasa ce kawai saboda muna muradin amfani da sojojinta".

Bayan Tchadi dai wata ƙasar sahara da zata yi tasiri a wannan yunkuri na amfani da ƙarfin soji a arewacin Mali itace Algeria, kamar yadda shugaban ƙasar Abdelaziz Bouteflika ya nunar a tattaunawarsa da sakariyar harkokin wajen Amurka Huilary Clinton, kwanaki kalilan gabanin taron na Bamako.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal