Taro a kan harkokin tsaro a Abuja
September 3, 2014Talla
Taron ana gudanar da shi ne musammun ma dangane da ayyukan ta'addanci da Najeriya ke fuskanta na 'yan Ƙungiyar Boko Haram da ke barazanar ƙwace yankin arewa maso gabashin Najeriyar.
taron wanda ke zaman na bita bayan taron Paris da aka gudanar a cikin watan Mayun da ya gabata, zai tattauna game da inda aka kwana a kan kawo ma ƙasashen na Afirka ɗauki da ƙasashen duniyar suka yi alƙawari domin yaƙi da ta'addanci.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu