Tariq Aziz ya rigamu gidan gaskiya | Labarai | DW | 05.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tariq Aziz ya rigamu gidan gaskiya

Mahukuntna kasar Iraqi sun sanar da mutuwar tsohon babban jami'in gwamnatin marigayi tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Saddam Hussein.

Tariq Aziz tsohon jami'an gwamnatin Saddam Hussein tshohon shugaban Iraqi

Tariq Aziz tsohon jami'an gwamnatin Saddam Hussein tshohon shugaban Iraqi

Rahotanni sun bayyana cewa Tariq Aziz mai kimanin shekaru 79 a duniya ya mutu ne a asibitin al-Hussein da ke birnini Nasiriyah a wannan Jumma'a. Aziz wanda kotun kasar ta Iraqi ta yanke masa hukuncin kisa bisa rawar da ya taka a gwamnatin Saddam Hussein da ta janyo asarar rayukan dubun-dubatar al'ummar kasar iraqin, kafin rasuwarsa yana tsare ne a gidan yari da ke arewacin kasar inda ya ke jiran a aiwatar da hukuncin kisan da aka yanke masa. Tun a shekara ta 2010 ne dai aka yankewa Aziz hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai dai har ya rasu ba a aiwatar da hukuncin da aka yanke masan ba.