Tarihin Sarki Bhumibol Adulyadej | Amsoshin takardunku | DW | 16.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Sarki Bhumibol Adulyadej

An haifi Sarki Bhumibol Adulyade a ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 1927 a wani asibiti da ke birnin Cambridge na jihar Massachussets na Amirka.

An haifi Sarki Bhumibol Adulyadej a ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 1927 kuma a wani asibiti da ke birnin Cambridge na jihar Massachussets na Amirka ne aka haife shi lokacin da mahaifinsa ke karatu a kasar ta Amirka. Bayan da ya shekara guda da haihuwa mahaifinsa da mahaifiyarsa suka koma da shi gida Thailand.

A kasar ta Thailand ne Sarki Bhumibol ya fara karatunsa na boko a wata makaranta da ake kira Mater Dei da ke binrin Bangkok, sai dai ya cigaba da karatunsa ne a kasar Switzerland daga shekarar 1933 lokacin da mahaifiyarsa ta koma can da zama bayan rasuwar mahaifinsa. A can Switerland din ne ya samu takardar shaidar digiri a fannin kimiya baya ga kwasakwasai da ya yi a fannoni da dama ciki kuwa har da harshen Farasanci. Bayan da aka kawo karshen yakin duniya na biyu Sarki Bhumibol da mahaifiyarsa da 'yan uwansa suka koma gida Thailand inda suka cigaba da zama kuma 'yan watanni bayan komawarsu gida ne wato shekarar 1946 aka nada shi sarki bayan da aka hallaka danuwasa wato Ananda Mahidol da ke rike da saurautar kasar. Kafin cikar kwanaki 100 na zaman makokin dan uwan nasa, Sarkin Bhumibol ya koma kasar Switzerland don kimtsawa sosai da nufin karbar mulki.

Thailand Bangkok - Beisetzung von König Bhumibol Adulyadej (picture-alliance/dpa/R. Yongrit)

Dubban 'yan Thailand sun yi ta shirga kuka bayan da suka samu labarin rasuwar Sarki Bhumibol Adulyadej

A ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 1950 ne Bhumibol ya hau gadon mulki bayan gagarumin bikin da aka yi na nadin sarauta kuma a jwabinsa da ya yi na karbar muki, sarki ya yi alkawarin jagoranci bisa adalci da kuma gaskiya da rikon amana. A wannan lokaci an gudanar da kasaitaccen biki kuma a wannan rana ce ya nada mai dakinsa Sirika a matsayin sarauniya.  A shekarun farko-farko na mulkinsa, Sarki Bhumibol bai da wani karfin fada a ji a harkokin mulki na Thailand hasalima ana daukarsa ne kawai a matsayin uban kasa don haka ba wani batu mulkin kasar da ake dama shi. Sai daga baya ya samu karfin fada a ji musamman ma fafutukar da rika yi wajen maida kasar kan tafarkin dimokradiyya. Hawa kujerar naki da ya yi kan amincewa da juyin mulkin soji da aka yi a kasar a shekarar 1981 da kuma 1985 na daya daga cikin abubuwan da suka sanya shi yin farin jini tsakanin al'ummar kasar.

Kayamar da Sarkin ke yi wa sha da safarar muggan kwayoyi ma dai ya sanya shi yin kima a idon 'yan kasar musamman ma da ya ke a wannan lokacin ne aka bukaci gwamnatin Thaksin Shinwatra da ta yi amfani da rinjayen da ta ke da shi a majalisa dokokin Thailand din don yin doka da za ta kafa kotu da zummar hukunta masu ta'amali da muggan kwayoyi, kuma a wannan lokaci ne wato a shekarar ta 2003 aka soma wani gangami na yaki da masu sha da fataucin kwayoyi. Daga shekarar 2006 da shidda ne yanayin lafiya na Sarki Bhumibol ya fara tabarbarewa abin kuma ya fara kamari a 2007 lokacin da ya kwanta a asibiti bayan da aka gano cewar yawan jinin da ke zuwa kwakwalwarsa ya gaza yadda ake bukata. Haka dai lamarin ya cigaba da wakana har zuwa tara ga wannan watan na Oktoba da muke ciki lokacin da likotoci suka ce ya cikin matsanancin hali, har an kai ga sanya shi kan na'urar da ke tallafa masa wajen yin numfashi.

Thailand Bangkok - Beisetzung von König Bhumibol Adulyadej (picture-alliance/AP Photo/W. Wanichakorn)

Al'ummar Thailand sun ce za su jima ba su mance da Sarki Bhumibol ba saboda irin salon mulkinsa

A wannan lokaci dai dubban 'yan kasar sun yi dafifi a gaban asibitin da ya ke kwance sanye da kaya ruwan hoda inda suke ta addu'ar samun sauki ga sarki. To amma wa'adinsa ya cika a ranar 13 ga wannan wata na Oktoba da misalin karfe hudu saura mintuna 8 na yammaci agogon kasar kamar yadda wata majiya daga fadarsa ta shaidawa al'ummarsa. 'Yan kasar dai sun yi takaicin rasuwar Sarki Bhumibol Adulyadej wanda shi ne sarki mafi dadadewa kan gadon mulkin kasar Thailand a halin yanzu. Makusanta dai sun ce mutum ne mai saukin kai kana ya na da sha'awa ta sauraron kidan Jazz kuma gwani ne na daukar hotuna.