Tarihin sabuwar Firaministar Birtaniya | Siyasa | DW | 13.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tarihin sabuwar Firaministar Birtaniya

Theresa May ce ta maye gurbin David Cameron a fadar mulki ta Downing street bayan rantsuwar kama aiki. Ita ce mace ta biyu da ta rike wannan mukamin Firaminista a kasar

Saurari sauti 03:00

Tarihin Theresa May, sabuwar Firaministar Birtaniya

Shin ko Theresa May ce sabuwar Margaret Thatcher, mace mai kamar maza ta biyu? Ita dai ba mace ce da za a iya juya ta cikin ruwan sanyi ba. Abu ne da kowa ya sani a kasar domin kuwa hatta rundunar 'yan sandan Birtaniya ta san da hakan, yayin da ta rike da mukamin sakatariyar harkokin cikin gidan.

Wani dan jam'iyyarta da ya yi aiki a karkashin Thatcher, ya bayyana Theresa May a matsayin mace mai tsattsauran ra'ayi. sai dai ya ce duk da haka tana burgeshi. Shi kuwa tsohon sakataren kudi na Birtaniyan Vince Cable, ya ce koda yake bata burgeshi kana ba ma jam'iyarsu daya ba, sai dai yana girmamata a masatyin mace mai jajircewa wajen ganin ta cimma nasara a dukkan abin da ta sanya a gaba.

Großbritannien Theresa May Statement

'Ya'yan Jam'iyyar Conservative su baiwa May goyon baya 100%

Cabel ya ce: "Tana da sanin makamar aiki kuma tana tsayawa kan manufarta. Misali kan batun bakin haure, mun ga irin matakin da ta dauka a kan baiwa dalibai takardar izinin shiga kasa wato Viza ta Birtaniya, ta soki ra'ayin sakataren kudi na Birtaniya da ma Firaminista david Cameron."

Banbani manufofi tsakanin Thatcher da May

Mai shekaru 59 a duniya, Theresa May za ta iya zama daban. Yayin da Margaret Thatcher ta yi kira kan habaka harkokin kasauwanci, kana aka yi watsi da kananan 'yan kasuwa, a shekara ta 2002 May ta bukaci da a sake inganta harkokin siyasa da tattalin arziki.

May ta ce "Ba wai mun yarda da kasuwa bane kawai, amma mun yarda ne da hadin kan al'umma. Ba wai mun yarda da mutane a dai-daiku bane, sai dai kasancewar al'umma a dunkule. Ba mu tsani gwamnati ba, kuma muna girmama rawar da gwamnati ce kadai za ta iya takawa. Kuma mun yi imanin ko wanne mutum ba wai tsirarun da suke da wata dama ba, na da damar su yanke shawara a kan abin da ya shafi rayuwarsu."

Wannan dai abu ne da Margaret Thatcher ba ta taba fada ba. Shin hakan na nufin cewa Theresa May, na da tsattsauran ra'ayi amma cikin saukin kai? Bayan da Birtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai EU dai, an yi ta yada jita-jitar cewa Birtaniya za ta kada kuri'a a karo na biyu, sai dai May ta musanta hakan a gaban dimbin magoya bayanta.

Großbritannien Theresa May kommt in Downing Street an

Theresa May ce mace ta biyu da ke shiga fadar Downing street

Ta ce " Ficewa daga Tarayar Turai na nufin ficewa, za kuma mu yi kokarin cimma nasarar hakan, babu wani yunkuri na ci gaba da zama cikin kungiyar EU."

Theresa May dai ta kasance daya daga cikin wadanda suka mara wa ci gaba da zaman Birtaniya cikin kungiyar Tarayyar Turai baya, gabanin kada kuri'ar raba gardamar da ta jagoranci ficewar Birtaniyan daga EU.

Sauti da bidiyo akan labarin