Tarihin Paparoma Benedikt na 16 | Amsoshin takardunku | DW | 05.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Paparoma Benedikt na 16

An haifi Joseph Ratzinger a shekara 1927 a garin Marktl am Inn dake kudancin Jamus, ya zama Paparoma Benedikt na 16 a shekara 2005.

Paparoma Benedikt na16 ainahin sunansa Joseph Ratzinger, kuma bajamushe ne, an haife shi ranar 16 ga watan Afrilu na shekara 1927 wato yanzu ya na da shekaru kusan 86 kenan a duniya.An haife shi awani gari mai suna Marktl am Inn da ke jihar Bavariya a kudancin Jamus.

Ma'aifinsa jami'an tsaro.Joseph Ratzinger ya yi kusan duk yarintarsa a wani gari mai suna Traunstein a nan ya fara shawar sadaukar da kai ga harkokin ibada , hasali ma a darikar Roman Katolika, wadda ita ce iyayensa su ke biya.

Yayi yarinta a lokacin da Hitler ke mulkin Jamus, kuma a wannan lokacin, masu akidar Nazi sun dora karen tsana ga mabiya darikar Katolika.Zamanin yakin duniya na biyu an cilasta masa shiga rundunar yakin dakarun Hitler,ya samu kansa daga wannan rundan bayan da Jamus ta yi saranda wato bayan da aka ci ta da yaki.

A fannin karatu yayi karancin ilimin falsafa da da kuma na addini a cibiyar koyarwa ta Freising da kuma a jami'ar Munich.

Ya samu digirin digirgir ta fannin ilimin addini a shekara 1953.

Yayi koyarawa jami'o'i daban-daban na Jamus kamar jami'ar Münster,Tübingen da ma jami'ar birnin Bonn daga 1959 zuwa 1963.

A nan birnin Bonn yayi zama wata unguwa da ke kira Bad Godesberg.

Yaushe Joseph Ratzinger ya shiga dagan-gadan cikin aiyukan ibada har ta kai shi ga matsayin Paparoma?

Joseph Ratzinger kamar yadda na baiyana da farko, ya fara shawara addini tun ya na da matashi, kuma bayan ya kamalla karatun firamare sai ya fara karance-karande na littafafen addini abinda ya bashi damar kurrewa ta fannin ilimin addini.

A karon farko ya zama a shekara 1951, kamin daga bisani ya yi ta samun daukaka a manyan mukamai na majalisar limaman kiristoci ta Jamus dalili da hazaka da kuma ilimin da Allah ya ba shi.

Saboda haka ne kuma Paparoma Jean Paul na 6 ya nada shi Atbishop na Roman Katolika a Jamus a shekara 1977.

Ratzinger shi da kansa ya kada kuri'a a lokacin da aka shirya zaben Paparoma Jean-Paul na II a watan Oktoba na shekara 1978.

A lokacin da aka zabi Jean Paul na biyu a matsayin Paparoma a shekara 1978, Joseph Ratzinger ya kara samun shiga domin cemma sun shaku da Jean Paul na biyu kuma ya san shi game da ilimi da ibada.

Daga wane lokaci ne Joseph Ratzinger ya fara aiki a fadar Vatican?

Bayan da aka zabi Karol Wojtila a matasayin Paparoma Jean- Paul na biyu a shekara 1978, shine ya yanke shawara dauko Joseph Ratzinger ya maido shi kusa da shi afadar Varican, saboda haka shi tamkar ministan dake kula da kare darikar Roman Katolika daga bidi'o'i da kuma kula da koyar da ka'idojin wannan ibada.

An nada shi wannan mukami ranar 25 ga watan Nowemba na shekara 1981 daga nan sai yayi murabus daga matsayinsa na Atbishop din Munich da Freising.

Dalili da wannan mukami da ya rike sai ya zama daya daga cikin na hannun damar Paparoma Jean-Paul na biyu domin ko wane mako sai sun hadu so biyu domin yayi masa bitar aiyuka.Ya rike wannan mukami tsawan shekaru 23.

Bugu da kari Paparoma Jean Paul na II ya kara vmasa wasu lambobin girma inda aka nada shi amatsayin jagora matasayin mataimaki na shugaban Majalisar Atbishop na fadar Vatican kamin daga baya ya zama shugaba.

A tsawan shekaru da dama Joseph Ratzinger ya walafa littatafai da dama wanda ke karin haske game da aiyukan ibadar Katolika.

Saboda wannan daukaka da ya samu bayan da Paparoma Jean Paul na II ya kwanta dama sai aka zabe shi a matsayin saban Paparoma ranar 19 ga watan Afrilu na shekara 2005.

An yi bikin rantsar da shi ranar 24 ga watan Afrilu na shekara 2005.

Bayan ya dauki wannan matsayi ne ya samu sunan Benedikt na 16.

Paparoma ya yi shekaru kusanTakwas ya na jagorancin darikar Roman Katolika.ya samu yabo matuka daga mabiya darikar Roman katolika na Duniya.

Ta banganren cude ni-in- cude ka da sauran addinai ma,Paparoma Benedikt n a16 ya taka mahimmiyar rawa.Misali a watan Nowemba na shekara 2007, ya hadu da Sarki Abdelah na Saudiyya wadda itace ganawa farko da aka taba yi tsakanin wani Paparoma da sarkin kasar Saudi Arabiya.Haka kuma ya sha kiraye-kirayen ta fannin fahintar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban, musulunci, yahudanci addinin Buda da dai sauran addinai.

Murabus din Paparoma Benedikt na 16:

Babu zato babu tsammani ranar 11 ga watan Faburairu Paparona Bebedikt na 16,ya kiri taron Atbishop na fadar Vatican inda ya basu sanarwar yin murabus daga wannan mukami.Ya ce a ranar 28 ga watan Faburairu na wannan shekara ta 2013 zai ajje aikin, ga ma dai kadan daga cikinjawabin da yayi:

"Ya ku 'yan uwa na gayyato ku a wannan taro domin in sanar da ku wata mahimmiyar shawara da na yanke.Bayan tunani da dogon nazari, bayan addu' o'i neman haske daga Uban Giji, na yanke shawara sauka daga mukamina na Paparoma saboda cutar tsufa.Wannan aiki ne da ke bukatar jini a jika, wanda a yanzu ba ni da shi.

Ina rokon Allah ya haskaka zukatanmu, mu zabi saban jagora.

Sauran shekarun da Allah ya yanke min a rayuta, zan saudakar da su wurin aiyukan ibada."

A tarihin darikar Roman Katolika,Benedikt na 16 shine Paparoma na farko da ya yi murabus daga mukaminsa a cikin shekaru kusan 600 da suka wuce.Bayan shi an ce akwai wani Paparoma mai suna Gregoire na XII wanda ya taba yin murabus amma bisa matsin lamba, a shekara 1415.

Banedikt na 16 ya gabatar da jawabin karshe ga mabiya darikar Roman Katolika dubu 150 da suka hadu a fadar Vatican ranar 27 ga watan Faburairu.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Saleh Umar Saleh