Tarihin Michel Djotodia | Amsoshin takardunku | DW | 08.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Michel Djotodia

Saban shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai shekaru 64 a duniya ya shiga tawaye tun 2005.

Chief of the SELEKA rebel alliance Michel Djotodia sits on January 17, 2013 in Bangui during a ceremony. Opposition figure Nicolas Tiangaye was officially appointed today Prime Minister of the Central African Republic's new national unity government, President Francois Bozize said after a ceremony in the capital Bangui. The announcement was in line with a peace deal struck between the ruling party, the Seleka rebels and the democratic opposition in the Gabonese capital of Libreville last week.

Michel Djotodia

Michel Djotodia an haife shi a shekara 1949 a wani gari mai suna Vakaga a gabar kogin Ubangi-Chari na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yanzu ya na da shekaru 64 a duniya.

Bayan ya yi karatu Firamare da Sakandare a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya tafi Tarayyar Soviet ko kuma kasar Rasha ta yanzu,inda ya share shekaru 14, ya yi karatu a fannin ilimin fasali.

Da ya dawo gida ya yi aiki a ofishin ministan fasali da kuma ofishin ministan harkokin waje, kamin daga bisani a nada shi karamin jakadan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a birnin Nyala na kasar Sudan

Djotodiaa na daya daga sojojin da suka jagorancin gwagwarmaya da shugaban Jamhuriya Afirka ta Tsakiya, François Bozize, a karkashin wata kungiyar tawaye mai suna, UFDR, kokuma "Union des Forces Democratiques pour le Rassemblement".Saidai kamin ya shiga tawayen saida ya yi takarar zama dan Majalisar har so biyu a mazabar Vakaga dake yankin arewa maso gabashin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, amma bai yi nasara ba.

Chadian soldiers wait on a truck near the Damara, the last strategic town between the rebels from the SELEKA coalition and the country's capital Bangui, on January 2, 2013, as the regional African force FOMAC's commander warned rebels against trying to take the town, saying it would 'amount to a declaration of war.' The rebels, who began their campaign a month ago and have taken several key towns and cities, have accused Central African Republic leader Francois Bozize of failing to honor a 2007 peace deal. AFP PHOTO/ SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

'Yan tawayen Seleka

Yaushe Michel Djotodia ya shiga tawaye har ya yi nasara kifar da shugaban kasa François Bozize?

Miche Djotodia ya shiga tawaye a shekara 2005 kuma ya na daga cikin wanda suka girka kungiyar tawayen UFDR.Wannan runduna ta kunshi kananan kungiyoyin tawaye wanda suka gama karfi domin hambbara da gwamnati.

Masu kula da al'amuran tawaye a kasar na cewa, zaman da yayi a Sudan ya bashi damar kulla huldodi da 'yan tawayen Sudan da na Chadi, tare da hadin gwiwarsu ne ya zama shugaban UFDR kuma ya sami makamai.

Dalili da matsin lambar da ya sa fuskanta daga gwamnatin François Bozize, cilas ya shiga gudun hijira tare da kakakinsa mai suna Abakar Sabone.Sun sami mafaka a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin a shekara 2007.Bayan tafiyarsa sai Damane Zakariya ya karbi jagorancin kungiyar tawayen UFDR.To saidai a watan Nowemba na shekara 2007 bisa bukatar shugaban François Bozize sai hukumomin tsaron Benin suka cafke Michel Djotodia da shi da kakakin nasa, kamin daga bisani a yi belin su,a watan Faburairu na shekara 2008, bayan amincewar da suka yi su halarci taron sulhu tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Bayan rattaba hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya,a shekara 2008 sai Djotodia ya koma da zama a yankin Kudancin Darfur na kasar Sudan kuma ana kwatanta cewa a wannan lokaci ne,ya kafa sabuwar kungiyar tawaye.

A shekara 2011 ne ya yi nasara hada kai kananan kungiyoyin tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wuri guda,tare da burin kifar da shugaban kasa da ya ke zargi da almubazaranci,da kama karya,da kuma babakere da dukiyar jama'a.Wannan sabuwar kungiyar tawaye da ya girka ya sa mata sunan Seleka wato "Hada ka" da yaren kabilar Sango da ake amfani da shi a kasar.

The Central African Republic's President Francois Bozize looks on as he gives a press conference, on January 8, 2013 at the presidential palace in Bangui. Bozize refused on January 8 to discuss resigning at upcoming peace talks with rebels who have stormed across the country and seized several key towns. AFP PHOTO/ SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

Hambarraren shugaba Francois Bozize

A kwana a tashi wannan kungiyar ta fara samun galaba kan dakarun gwamnati, inda cilas aka sake zama tsakanin 'yan tawayen Seleka da gwamnatin Jamhuriya Afirka ta Tsakiya da kuma 'yan adawa birnin Libreville na kasar gabon a watan Janairun wannan shekara ta 2011, an cimma yarjejeniyar da ta kunshi matakai da dama.A gwamnatin hadin kan kasa da aka girka, sakamakon yarjejeniyar Michel Djotodiaa ya zama ministan tsaron kasa bugu da kari mataimakin Firaminista.

Saidai tafiya ba ta yi nisa ba, 'yan tawayen suka zargi shugaba François Bozize da rashin mutunta yarjejeniyar Libreville saboda haka su ka koma fagen daga har dai daga karshe su ka yi nasara kwace mulki a watan Maris na shekara 2013 kuma ya nada kansa shugaban kasa.A cikin gwamnatin da ya girka shi ya ci gaba da rike matsayin ministan tsaro kuma shugaban kasa.

Yayi alkawarin zai sauka daga kujera mulki nan da shekaru ukku masu zuwa bayabn ya shirya zaben demokradiya cikin tsafta, to saidai a zuuba ido a ga ko zai cika alkawari kokuma a'a.Tuni ya fara fusknatar cikas domin 'yan adawar kasar sun kaurace daga gwamnatin da ya kafa tare da zargin cewa 'yan tawayen Seleka sun mamaye duk mukamai masu tsoka, sun mikawa sauran mukamai irin na jeka na yi ka.

Da gaske ne wai Michel Djotodiaa musulmi ne?

Kwarai da gaske Michel Djotodia musulmi ne.

Partisans of new Central African Republic leader Michel Djotodia hold flags and banners during a support march in the streets of Bangui on March 30, 2013. The Central African Republic's new strongman Michel Djotodia vowed Saturday not to contest 2016 polls and hand over power at the end of the three-year transition he declared after his coup a week ago. (banner reads; 5th districj, Banda-GB quarter, Yes to change, Support the President Michel Djotodia Am Nondroko '). AFP PHOTO / SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)

Zanga-zanga a Bangui

Wannan shine karon farko da aka taba samun shugaban kasa musulmi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Ga wanda suka kalli fitar sa ta farko bayan da ya karbi mulki daga Francois Bozize ya yi ta ne zuwa masalcin juma'ar Bangui babban birnin kasar inda yayi sallar juma'a.

Sannan a cikin hirraraki da 'yan jarida ya maida martani ga masu zarginsa da kasancewa mai tsatsauran kishin addini Islama, ya ce lalle shi musulmi ne amma ba shi da ra'ayi irin na mabiya kungiyoyi masu tsatsauran kishin addini kamar su AQMI, sannan a cikin wannan baiyana ya yi alkawarin cewar zai gudanar da shugabancin cikin adalci ba tare da la'akari da addinsa ba.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman