Tarihin masarautar Katagum | Amsoshin takardunku | DW | 17.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin masarautar Katagum

Ita dai masarautar Katagum tana jihar Bauchi a Tarayyar Najeriya ne, kuma daya ce cikin masarautu da suka karbo tutar Shehu Usumanu Danfodiyo.

Masarautar a yanzu ta tashi daga garin Katagum inda nanne ainihin tushen ta, lokacin da almajirin Shehu Usumanu Danfodiyo wato Malam Ibrahim Zaki ya karbo tuta kuma ya kafa masarautar, amma yanzu ta dawo cikin garin Azare. Sai dai har yanzu tana amsa sunan Katagum, ko da yake garin Katagum din a yanzu hakimi ne ke iko da shi, wato Galadiman Katagum. Kuma Katagum shi ne ke zaman helkwatar karamar humar Zaki a jihar Bauchi. A yanzu dai DR Muhammadu Kabiru Umar shi ne ke kan kujerar mulkin sarauta, wanda ya karba bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 1980. Don jin karin bayani ana iya sauraron sauti a kasa cikin hirar da DW ta yi da Turakin Katagum, Alhaji Muhammadu Gadauji. Bayaga tarihin Masarautar Katagum, akwai kuma cikakken tarihin sarkin Katagum na yanzu:

Akwai kuma tarihin dan takaran shugabancin Jamhuriyar Nijar wato Hama Amadou da kuma abin da dokar Najeriya ta fada kan tafiyar hutun shugaban kasa. Duk ana iya saurar a cikin sautin da ke kasa.

Sauti da bidiyo akan labarin