Tarihin jiragen sama marasa matuka | Amsoshin takardunku | DW | 25.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin jiragen sama marasa matuka

Jiragen sama marasa matuki an fara amfani da su tun kafin zuwan jirgin sama domin kai hari kan abokan gaba.

Kasar Ostiriya (Austria) da ke nahiyar Turai ta fara amfani da jirkin sama da babu matuki a shekarar 1849, inda kasar ta yi amfani da wani abu mai kama da balo-balo kimanin guda 200 aka saka musu bama-bamai sannan aka jefa wani garin Venice na kasar Italiya.

Sannan daga bisani kasar Amirka ta yi amfani da irin wannan yayin yakin basasa na kasar, kuma yanzu haka kasar ke kan gaba wajen amfani da wdaanda jiragen sama marasa matuki a wurare daban-daban na duniya, musamman a kasashen PPakistan, da Afghanistan da kuma wasu sassa da duniya da suka hada da Afirka.

Yanzu akwai jiragen marasa matuka da ke aikin tattara bayanai na sirri, sannan wasu kuma ana amfani da su wajen kai hare-hare musamman kan kungiyoyi masu nasaba da ta'addanci.