Tarihin Hugo Chavez | Amsoshin takardunku | DW | 11.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Hugo Chavez

An haifi Hugo Rafael Chavez Frias ranar 28 ga watan Juli na shekara 1954 a Sabaneta cikin jihar Barinas dake kudancin ƙasar Venezuela

Venezuelan President Hugo Chavez salutes during a military ceremony in the National Army Academy in Caracas on November 6, 2011. AFP PHOTO / Leo RAMIREZ (Photo credit should read LEO RAMIREZ/AFP/Getty Images)

Hugo Chavez

Hugo Rafael Chavez Frias,da 'yan Venezuela ke kira "Kommadante" an haife shi ranar 28 ga watan Juli na shekara 1954 a wani gari mai suna Sabaneta a cikin jihar Barinas dake kudancin Venezuela, wato kamin rasuwarsa ya na shekaru kusan 59 a duniya.Iyayensa maluman makaranta ne, amma kuma mahaifinsa so ukku ya na zama gwamna jihar Barinas.

Hugo Chavez ya shiga firamari a garin Sabaneta, kamin daga baya ya shiga makarantar sakandare a Barinas.Tun ya da ƙuruciya yaro ne mai karambani kuma mai shawar wasan motsa jiki.

Ya ci gaba da karatu a jami'ar Simon Bolivar da ke Karakas babban birnin Venezuela amma bai kammala karatun ba, sai ya shiga soja a yayin da ya samu shekaru 17 a duniya.

Ranar 24 ga watan Juli na shekara 1983, wanna rana ce aka yi bikin cikar shekaru 200 da aihuwa wani gwarzo mai suna Simon Bolivar wanda shine Hugo Chavez ke koyi da shi.

Venezuelan President Hugo Chavez holds a Spanish language version of Hegemony or Survival: America's Quest for Global Dominance by Noam Chomsky while addressing the 61st session of the United Nations General Assembly at U.N. headquarters on Wednesday Sept. 20, 2006. (AP Photo/Julie Jacobson)

Bolivar shine ya jagorancin gwagwarmayar ƙwatar 'yancin ƙasashen yankin Latine Amurika daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Spain.

Chavez da wasu abokansa sojoji sun girka wata ƙungiya da suka raɗawa suna ƙungiyar juyin juya halin mai aƙidar Bolivar.A ƙarƙashin wannan ƙungiya bisa jagorancin Hugo Chavez sojojin suka yi yunƙurin hamɓarra da shugaba Carlos Andres Perez daga karaga mulki ba tare da narasa ba.

Saboda haka sai a kame shi aka tura shi kurkuru tsawan shekaru biyu.Daga cikin kurkukun Chavez ya shirya wani jawabi ta faifen Vidio inda ya kiri al'umar Venezuela ta burjinewa hukuma domin ta ƙwaci 'yanci.Daga wannan lokacin ya fara samun farin jini a Venezuela.

Shekaru biyu bayan kulle Hugo Chavez sai aka shirya zaɓen shugaban ƙasa inda aka zaɓi Rafael Caldera, wanda kuma shine ya bada umurcin belin Chavez daga kurkuku.Tun daga wannan lokaci sai ya kafa jam'iyar siyasa, wada a ƙarƙashinta ta lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekara 1999, kuma tun daga wannan lokaci ya ke ta yin tazarce.A lokacin da ya rasu an zaɓe shi karo na huɗu bai ma kai ga rantsar da shi mai ɗauka ta ɗauka bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya.

Saidai a lokacin mulkinsa duk da farin jinin da ya samu daga jama'ar ƙasa, ya kuma fuskanci ƙalubale mai yawa daga 'yan adawa, domin saida ma a ka kifar da shi ta hanyar juyin mulkin a shekara 2001, amma bayan kwanaki biyu kuma ya dawo karagar mulki.

Dalilan da su ka sa Hugo Chavez ya samu farin jini daga al'umar ƙasar Venezuela.

Babban dalili shine siyasar da ya shimfiɗa ta tausayawa talaka da kuma ba talakawa damar faɗin albarkacin bakinsu game da harkokin da suka shafi tafiyar da ƙasa.Misali ta fannin kiwon lafiya magani kyauta ruwan Allah ko wane ɗan ƙasa ke samu idan ya tsinci kansa cikin halin rashin lafiya.Bangaren makaratun komi kyauta ne, haka kuma kuma ta ko wane fanni na rayuwa shugaban Hugo Chavez na amfani da magudan kuɗaɗe da ƙasar ke samu ta hanyar cinakin man fetur domin taimakawa talakawa.Cemma talaka abinda ya ke so shine ya ci ya sha, ya samu magani da karatu da dai sauran ababen more rayuwa, to duk wannan gwamnatin Hugo Chavez ta na kulawa da su.

Duk da cewar akwai suka kwarai da ya ke samu daga 'yan adawa wanda ke zargin gwamnatin da cin hanci da rashawa da kuma facaka da kuɗaɗe.

Gaba tsakanin Hugo Chavez da ƙasashen yammacin duniya, mussamman Amurika.

Babban dalili shine bambancin aƙida da tafiyar da al'amuran shugabacin tsakanin Venezuela da wannan ƙasashe.

Samun cikkaken 'yanci na daga ginshiƙan da Chavez yayi dogaro da su, saboda haka ne ma ya kori duk kamfanonin da ke hakar man fetur a ƙasar wanda ya dangata da macuta.

ga abinda ya ce a lokacin:

" Ku tafi ku bamu wuri, daga yanzu ƙasarmu da yankin Latine Amurika gaba ɗaya, mun daina zama saniyar tatsarku.Kun kasance tamkar kaska a jikinmu, kuna tsotse jinin mu da arzikin da muka mallaka, daga yau wannan ta ƙare"

Wannan mataki da ya ɗauka ya ƙara dagula dangantaka tsakanin Venezuela da ƙasashen Turai da Amurika.

Argentina's President Cristina Fernandez (L), her Uruguayan counterpart Jose Mujica (2nd L) and her Bolivian counterpart Evo Morales (2nd R) stand next to the coffin of late Venezuelan President Hugo Chavez during a wake at the military academy in Caracas March 6, 2013, in this picture provided by the Miraflores Palace. Authorities have not yet said where Chavez will be buried after his state funeral on Friday. REUTERS/Miraflores Palace/Handout (VENEZUELA - Tags: POLITICS OBITUARY TPX IMAGES OF THE DAY) ATTENTION EDITORS- THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS. FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS

Gawar Hugo Chavez

Idan ba a manta ba akwai wani taron shekara-shekara da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya inda Hugo Chavez ya ɗauki magana ya dangata shugaban George Bush na Amurika da sheɗani:

Hugo Chavez ya kalli Bush cikin tsabar idanu ya ce da shi ku kale shi , ku kalle shi, shine babban sheɗani a duniya, wanda ke hana ruwa gudu wajen samun zaman lafiya.

Sannan ya kasance manyan abokan Hugo Chavez sune kasashen da Amurika da Turai ke zaman gaba da su, kamar su Kuba, Rasha, Libiya Iran.An sha samun samun saɓani.

A shekara 2009 lokacin da Isra'ila ta kai wasu hare-hare a zirin Gaza, Hugo Chavez ya kori jikadan Isra'ila a Karakas a wani mataki na maida martani da harin da ya dangata da rashin imani, sannan kuma yayi Allah wadai game da yadda ƙasashen yammacin duniya ke kallon Isra'ila na cin karenta babu babbaka a Palestinu.

Rashin lafiyar Hugo Chavez:

Chavez yayi kusan shekaru biyu ba shi da koshin lafiya.

An yi masa aiki tiyarta na farko a ranar 10 ga watan Juni na shekara 2011 a ƙasar Kuba cikin sirri, sai daga baya shi da kansa ya bada labarin rashin lafiya tasa.Wata guda bayan anan a ka sake yi masa tiyata.da ya dawo ya ce ya warke sarai, saboda haka ne man ya shiga takara zaɓen shugaban ƙasa a watan Oktoba na shekara 2012, to amma an ci gaba da jita-jita game da rashin lafiyar ta sa.

Bayan cutar kansa da ya ke fama da ita sai kuma ya fuskanci matsala wajen yin sheka, cilas ya sake komawa a Kuba, a watan Disemba na shekara 2012, to saida cemma kamin ya tafi kamar ya san ba zai iya dawowa bisa karagar mulki ba , ya bar wasiya, inda ya buƙaci jama'a ta bada haɗin kai ga mataimakinsa, Nicolas Maduro domin ya ci gaba da aikin da ya fara.

Venezuelan Vice President Nicolas Maduro looks down at the presidential sash as National Assembly President Diosdado Cabello puts it on during his swearing-in ceremony as caretaker president following the death of President Hugo Chavez in Caracas March 8, 2013. Acting Venezuelan President Nicolas Maduro said on Friday he had asked the country's election authority to call an immediate vote to choose a successor for the late Chavez. REUTERS/Jorge Silva (VENEZUELA - Tags: POLITICS)

Nicolas Maduro shugaban Venezuela na riko

Da yake ƙasar na Venezuela bayan watani biyu kwance asibitin ƙurraru ta ƙasar Kuba Chavez ya dawo Karakas inda ya ce cigaba da jinya, har zuwa ranar biyar ga watan Maris na shekara 2013 inda ya kwanta dama. Mataimakin shugaban ƙasar Nicolas Maduro, ya bada sanarwar cikin kuka, ya na cewa:

" ya ku al'umar Venezuela na zo maku da wani mummuman labari. a A wannan Talata, "Kommandante" Hugo Chavez,ya kwanta dama a ƙarhe huɗu da minti 25, bayan ya fi fama da rashin lafiya kusan shekaru biyu.Allah jiƙan "Kommandante".

To hausawa ke cewa ko wane mai rai mamaci ne,a yanzu gaba daya hankalu sun karkakata ga zaben saban shugaban kasa wanda zai maye gurbin marigayi Hugo Chavez.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal