Tarihin Dalai Lama | Amsoshin takardunku | DW | 29.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tarihin Dalai Lama

Taƙaitacen tarihin Dalai Lama shugaban addinin Budah kuma shugaban gwamnatin gudun hijira ta yankin Tibet

Dalai Lama

Dalai Lama

Dalai Lama a yanzu shine shugaban addinin Budah na Tibet, yanki da ke buƙatar ɓallewa daga ƙasar China.

Sunansa na aihuwa shine Lhamo Dhondub, kuma an haife shi ranar shidda ga watan Juli na shekara 1935,a wani gari mai suna Taktser,a yankin na Tibet, kenan yanzu ya na da shekaru 75 a duniya.

Tun ya na dan shekaru biyu da aihuwa bisa al´ada al´umar Tibet,masu aruwa da sufaye su ka gano wasu mu´ujizoji tare da shi, saboda haka su ka yanke shawarar cewar shi, zai gaji shugaban addinin Budha na 13.Kuma daga wannan lokaci a ka raɗa masa suna Tenzin Gyatso.

An yi bikin naɗa Tenzin Gyasto Dalai Lama na 14 ranar 22 ga watan Fabuari na shekara 1940 ,wato shekaru biyar bayan aihuwar sa.

A yarensu ana nufi da Dalai Lama gulbin adalci.

Tun ya na ɗan shekarau shidda a ka kai shi wani gidan ƙisƙadi, inda ya koyi ƙabli da ba´adin ibadar addinin Boudha.Ya kammala duk wannan karatu a lokacin da ya samu shekaru 23 a duniya.

Tun shekara 1959 wato shekaru 51 kena da Dalai Lama ke cikin zaman gudun hijira a ƙasar Indiya.Ya bar Tibet bayan da ƙasar China ta kai wani samamen kan mai uwa da wabi a yankin Tibet sakamakon zargin da ta ke yiwa Dalai lama na shirya maƙarƙashiyar ɓalle Tibet daga ƙasar China.

Bayyanai sun nuna cewa ɗaruruwan limaman Boudha da wuraren ibadar u aka yiwa kacakaca a lokacin kai harin.

Ganin haka shi ya san Dalai Lama ya tsere zuwa Indiya, inda daga cen ya girka gwamnatin Tibet na gudun hijira, kuma ya samu karbuwa daga mabiya addinin Boudha, domin dubunan ɗaruruwan mutane sun tarda shi a Indiya inda su ke raye tare da shi.

A yanzu haka ya na zaune a wani gari mai suna Dharamsala da ke Indiya, kuma ya kan gudanar da tafiye tafiye a manyan ƙasashen duniya, mussamman Turai da Amirka , da suna shugaban gwamnatin yankin Tibet, da kuma matsayinsa na babban limamin addinin Boudhah, sai dai duk ƙasar da ya ziyarta, ta kan fuskanci fushi, daga hukumomin China, wanda su ke ɗaukar yankinTibet a matsayin mallakarsu, kuma su ke wa Dalai Lama kallon wani shugaban ´yan aware.

Dala-Lama ya samu kyautar Nobel ranar 10 Disemba na shekara 1989, wace a lokacin da ya cika shekaru 30 na gudun hijira.

Komitin da ke bada wannan lambar yabo, ya ce ya yi hakan ne domin ƙara ƙarfin gwiwa ga yunƙurin Dalai Lama na samar da zaman lafiya tsakanin yankin Tibet da China, ta hanyar tattanawa a madadin amfani da tsinin bindiga.

Kuma wannan lambar da ya samu ta ƙara ƙwazo ga mabiya addinin Budha na Tibet, sannan ta ƙara zabbura da ƙasashen duniya, wajen neman mafita ga rikici tsakanin Chine da yankin Tibet.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed Tijani Lawal