Tarayyar Afirka ta bukaci kyale 'yan agaji yankin Habasha
September 3, 2021Talla
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci gwamnatin Habasha ta dauki matakan tabbatar da cewa kungiyoyin jinkai sun samu shiga yankin Tigray domin kare mutane daga matsanancin yunwa, sakamakon rikicin da ke faruwa a wannan yankin.
Yankunan arewacin kasar sun fada cikin rikici a watan Nowamba da ya gabata lokacin da gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed ya tura sojojin da suka kawo karshen gwamnatin yankin na Tigray karkashin TPLF, sakamakon harin da aka kai kan sansanin sojojin gwamnatin tarayya a yankin. Akwai zargin duk bangarorin da ke rikici na kasar ta Habasha ana zargi da cin zarafin fararen hula.