Taraba: An shawo kan rikicin garin Wukari | Labarai | DW | 08.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taraba: An shawo kan rikicin garin Wukari

Sao'i bayan sanar da hukuncin kotun zabe na cewar Senata Aishatu Jummai Alhasan ce ta lashe zaben gwamnan jihar Taraba ne, fada ya barke a garin Wukari.

Rahotanni daga Wukari na jihar Taraba na cewa wata tarzoma ta barke a garin tun a daren jiya jim kadan bayan da wani hukunci kotu ya ce Senata Aisha Alhasan ce ta lashe zaben gwamna a jihar. Wakilin DW a Yola Muntaqa Ahiwa wanda ya isa a cikin jihar ta Taraba, ya ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen garin sun tabbatar masa da cewa, da tsakar daren jiya an ji harbe-harben bindigogi.

Wannan rikici dai ya yi sanadiyyar rayukan mutane, da kawo yanzu babu cikakken adadi, daura da asarar dukiyoyi sakamakon ko-konen da aka ayi.

Sai dai ya ce ya zuwa safiyar wannan Lahadi kura ta lafa bayan da aka kai jami'an tsaro a garin.