Tantance gaskiyar Labari kafin yada shi | Himma dai Matasa | DW | 18.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Tantance gaskiyar Labari kafin yada shi

Tantance gaskiya daga karya ba abu ne mai sauki ba. Ko da ya ke 'yan jarida masu muradin kare mutuncinsu, na ganin cewar hakan ya zama wajibi.

Tantance gaskiyar labari kafin yada shi.

Tantance gaskiyar labari kafin yada shi.

"Africa Check" kungiya ce mai zaman kanta wadda aka kafa a kasar Afrika ta kudu a shekara ta 2012 domin inganta mahawarar tabbatar da gaskiya tsakanin jama'a da kafofin yada labaran Afirka. Manufar aikinta shi ne tabbatar da cewar jama'ar Afirka sun samu bayanai na gaskiya. Ko da kunan tattara labarai na fuskantar matsala wajen tantance labaran gaskiya daga na karya, bibiyar labari don tabbatar da sahihancinsa wajibi ne ga 'yan jarida masu muradin kare martabar aikinsu. Mai gabatar da labarai Iman Rapetti daga talabijin na ENCA a Afrika ta kudu na sane da wahalar aikin jarida. Misali abu mai sauki ne a gaskata karyar da 'yan siyasa ke yi idan har ba a yi bincike ba. Akan haka ne Iman ta ke amfani da "Africa Check" a matsayin makaminta na sirri wajen tantance gaskiya ta Internet.

"Hukuma irin wannan na taimakawa wajen binciken sahihancin bayanai ko da kuwa an kammala shi. Hakan na bamu damar yin nazari daga inda muka samo bayananmu da yadda za mu yi amfani da shi"

Anim van Wyk na aiki ne da wannan kungiya mai zaman kanta da ake kira "Africa Check" a birnin Johannesburg. Ita da tawagarta sukan gudanar da bincike kan tabbatar da gaskiyar bayanai da ake gabatarwa jama'a. Ta wannan bincike da suke gudanarwa wajen tsame gaskiya daga karya ne, ba tare da nuna banbanci ba, kungiyar ta samu gindin zama tare da yin kima a idanun jama'a.

"Muna iya kokarinmu wajen kare kimar kungiyarmu ta hanyar nuna adalci a irin rahotanninmu. Muna daukar lokaci wajen bincika dukkan sassan muhawara na jam'iyyun siyasa, saboda kada mutane su ce muna adawa ko goyon bayan gwamnati ko 'yan adawa. Manufarmu ita ce tantance gaskiya kawai".

Afrika Check na da ofisoshinta a biranen Johannesburg da London da kuma Dakar fadar gwamnatin ksar Senegal. Kungiyar na samar da labarai a harsunan Turanci da Faransanci. Bugu da kari kungiyar na kuma aiki a Najeriya da Zambia da Zimbabwe. "Afrika Check" na samun tallafi daga cibiyoyi masu zaman kansu da asusun masu fafutukar ganin an tantance gaskiya daga karya da aikin jarida mai zaman kansa. Wanda ke nufin aikin Anim van Wyk ba mai sauki ba ne.

Sauti da bidiyo akan labarin