Tandja Mamadou mutum ne da ya rike mukamai da dama lokacin da ya ke soja kafin ya shiga fagen siyasa.
Daga cikin irin mukaman da ya rike har da gwamna da minista da shugabanci na ma'aikatu da dama. Ya kuma shugabanci Nijar karkashin jam'iyyar MNSD Nasara tsakanin shekarar 1999 zuwa karshen 2009.