May 30, 2018
Talla
Iman Dr Mohammad Nuraini Ashafa wani malamin addinin Islama a Najeriya ya bada amsar wadannan tambayoyi kan azumi. Sai kuma wasu tambayoyin da suka hada da shin meyasa shugaban kasa idan ya yi kasafin kudi idan 'yan majalisu ba su sa hanu ba, mai zai kasance? Domin samun amsa wannan batun DW ta tuntubi Dr. Aminu Umar masanin harkokin siyasa na kasashe duniya a Najeriya.
Sai kuma tambaya zuwa ga kwararrun likitoci: Wadanne irin kwayoyin cututtuka ne ake dauka daga shigowar farko-farkon Damuna?Wane irin hatsari ne Cututtukan suke haifarwa ga rayuwar bil adama? Wadanne irin hanyoyin rigakafi ne ya kamata iyaye su dauka dan kare kananan yara? amsa wannan tambayar za a ji daga bakin Dr. Zainab Mohammed, wata likita a garin na Kaduna.