Wace rawa masarautun gargajiya ke takawa wajen kare tarihin al'uma daga barazanar bacewa saboda zuwar zamani da ke sanya tarihin ke neman bacewa? Alhaji Usman Dalhatu, masanin tarihin al'adun Zazzau ya bayar da amsa.
Me masarautun gargajiya ke yi wajen magance rigingimun kabilanci da addinai da ke shafar zamantakewar mabanbantan kabilu da addinai? Tarihin al'umna da kabilu daban-daban a yankin arewacin Nigerian na ci-gaba da fuskantar kalubale, wacce shawara za a bayar wajen kare tarihin al'umma daga bazanar bacewa saboda rawar da zamani ke takawa wajen neman kawar da wasu Tarihi? Tambayoyin da Mr Anthony Hassan Audu da Mr Paul Danlami, mazauna garin Barnawa a Kaduna a Najeriya suka turo ke nan
Domin jin amsar wadannan tambayoyi wakilinmu Ibrahima Yakubu na Kadunan ya tattauna da Alhaji Usman Dalhatu, kwararren marubucin littattafan tarihin masarautun jihohin arewacin Najeriya,har wa yau kuma, masanin tarihin kayayyakin al'adun gargajiya na yankin arewa daga masarautar Zazzau