Tallafin Turai ga warware rikicin Mali | Labarai | DW | 19.11.2012
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tallafin Turai ga warware rikicin Mali

EU ta nuna goyon baya ga shirin tallafawa Mali domin murƙushe 'yan tawaye.

Ministocin kula da harkokin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai sun yi marhabin lale ga shirye-shiryen taimakawa shirin bayar da horo ga dakarun ƙasar Mali da nufin kawar da mayaƙan da suka karɓe iko da yankin arewacin ƙasar. Ƙasashe mambobin ƙungiyar ta EU, waɗanda suka gudanar da taron su a birnin Brussels, da ke zama cibiyar ƙungiyar tarayyar Turai - a wannan Litinin, sun amince da ƙoƙarin sake fasalin rundunar sojin ta Mali, tare da yin ƙira ga hanzarta kammala shirin domin amincewa da shi - nan da watan Disamba.

Tunda farko dai gwamnatin wucin gadin ƙasar ta Mali ta buƙaci samun tallafin ƙetare, inda ƙungiyar cinikayya ta yankin yammacin Afirka, ta ECOWAS da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya ke haɗa hannu wajen tsara rundunar kiyaye zaman lafiya a ƙasar.

Ministocin ƙasashen Turai ɗin dai suka ce akwai buƙatar fayyace wurin da zai kasance cibiyar rundunar - daga cikin ƙasashen da ke makwabtaka da ita Malin, da kuma buƙatar bada kariya ga sojojin Turai da ke bayar da horo ga dakarun na ƙasar Mali. Akan hakane, taron ministocin na EU ya buƙaci ƙasashe mambobi da su bayar da gudummowar su ga shirin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman

 • Kwanan wata 19.11.2012
 • Mawallafi Umar Saleh Saleh
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16m0J
 • Kwanan wata 19.11.2012
 • Mawallafi Umar Saleh Saleh
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/16m0J