Tallafin jihar Gombe ga ′yan gudun hijira daga Borno | Zamantakewa | DW | 31.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tallafin jihar Gombe ga 'yan gudun hijira daga Borno

A maimakon gina matsugunnai na wucin gadi a kan tituna, gwamnatin jihar Gombe ta baiwa masu gudun hijirar wani sansani dan rage musu irin kalubalen da suke fiskanta

A wani mataki na saukakewa dubban ‘yan gudun hijira da ke kwararowa daga jihar Borno saboda tabarbarewar tsaro gwamnatin jihar Gombe ta samar da wani sansani tare da samar da tallafi ga ‘yan gudun hijirar wanda a baya ke zube a kan hanyoyi da tashoshin mota.

Tun bayan da hare-haren kungiyar da aka fi sani da Boko Haram suka zafafa a yankunan jihar Borno al'ummomin wannan yankin suka kauracewa garuruwan su zuwa wuraren da suke ganin tudun na tsira ne kafin samun sauki su koma garuruwan su.

Ko a makon da ya gabata hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ta fidda alkaluma da suka nuna cewa akwai ‘yan gudun hijira sama da dubu goma sha biyar da suke tsere daga sassan jihar Borno zuwa jihohin da garuruwa makobtan jihar don neman mafaka.

Saboda kwararowar 'yan gudun hijira zuwa Gombe hukumomin suka tanadar da sansani don tsugunar da wadan nan bayin Allah wadanda a baya ke zube a kan hanyoyi ko tashoshin motoci wani lokaci ma har rowan sama na dukan su.

Dr Danlami Arabs Rukuje shine shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Gombe.

Yanzu haka akwai kusan ‘yan gudun hijira sama da dubu bakwai a wannan sansani inda ake sa ran karuwar wasu ‘yan gudun hijirar. Ziyarar da na kai wannan sansani naga mata da yara gami da magidanta sun kuma bayyana min halin da suke ciki da kuma irin tallafi da suke nema.

Alamu dai na nuna cewa tallafi da hukumomi suke kaiwa ‚yan gudun hijirar ba iya wadatarwa ba abinda ya sa ake kira ga kungiyoyi da sauran masu hannu da shuni da su aike da na su irin gudumowar don ragwa mutanen radadi da suke ciki.

Mawallafiya: Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita: Pinado Abdu Waba