Tallafin Amirka ga rikicin Mali
February 23, 2013Talla
A wani mataki na marawa dakarun Faransa da ke Mali baya, Amurka ta girke wasu jiragenta marasa matuƙa a maƙociyarta Nijar kamar yadda wata majiyar gwamnati a fadar White House ta bayyana, jiragen suna babban birnin ƙasar wato Yamai inda ta girke wasu ɗaruruwan dakarun sojin samanta.
Burin shine waɗannan jirage su sanya ido a yankin arewacin Mali inda faɗar ta fi ƙamari. Tun a tsakiyar watan Janairu dakarun Faransa suka shiga Malin dan yin aiki da dakarun yammacin Afirka wajen yaƙi da ƙungiyoyin ta'addan da ke tada zaune tsaye a ƙasar ta Mali
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi